Ikraam 15
Ikraam~ By Khaleesat Haiydar 15…… Ikram na xaune gaban Yakumbo da daddare bayan sun gama cin abinci tana mata fada ssae kan rashin ji da gantalin da take yi, Ikram sae tabe baki take tana jujjuya kwanon tuwan da ta gama ci, yakumbo tace “dubi fa don tsabar gantalinki da rashin ji Rabi har gida yan yankan kai suka xo nemanki” Ikram ta xaro manyan idanuwanta a tsorace tace “su waye yan yankan kan yakumbo?” Yakumbo tace “ahaf ae wa enan mutanen da suka xo gidanku daxu yan yankan kai ne” Ikram tace “wa ya gaya maki, matar fa na da kirki nasanta kuma har ayaba tana bani kuma ta taba kai ni katon gidansu” Yakumbo na girgixa kai tace “wayyo yarinya, ae daxun nn babanki da na lado suka je gidan suka ga ashe wae yara take dauka ta kai su bayan gidanta ta yanke kansu tayi kudi da shi” Ikram ta matso kusa da ita a tsorace tace “kice wllh yakumbo” Yakumbo tace “au da ke baki sani ba ae shi yasa mamarki ta dauko ki da gudo tana kuka ta taho dake nn,” Ikram kmr xata yi kuka tace “wllh kuma ta taba bani ayaba naci, kai na baxae fita ba yakumbo?” yakumbo tace “yo sae dae muyi ta maki addua idan Allah yasa kan xae tsaya” kuka Ikram ta fashe da ta xube jikin yakumbo jikinta na rawa tace “don Allah yakumbo kar kai ne ya cire wllh ina sonsa” yakumbo ta danne dariyarta ta rungumota tace “ae xan ta yi maki addua yau cikin dare idan Allah ya yrda baxae cire ba, Allah ya fita” Ikram bata sake cewa komai ba tayi lamo jikin yakumbo jikinta na rawa tana ta tunane tunanen abinda Mami ta taba bata taci, har bacci ya dauketa, yakumbo ta kwantar da ita tace “ja’ira kawae, ae abinda Aisha ya kamata ta dinga maki knn ta kasa kullum tayi ta jibgarki kmr jaka” fitilar dakin yakumbo ta rage ita ma ta kwanta bayan ta tura masu kofa, ranar dae yakumbo bata yi baccin kirki ba don ihu ikram ta dinga mata cikin dare wae gasu nn xasu cire kanta, da kyar yakumbo ta samu tayi bacci kusan asuba tana to fa mata addua, ko kadan bata yi da ta sanin tsoratata da tayi ba don a ganinta hkn xae sa ta nutsu. Washegari ko ta tashi da xaxxabi ssae, to nn fa hnklin yakumbo ya tashi, ta bata koko ta sha kadan shima da kyar snn ta bata magani ta kwanta, kin fita ko nn da tsakar gida Ikram tayi ranar, yakumbo taji ddi ssae, ashe dae akwae abinda xae sa Ikram ta ki fita ko nn da tsakar gida. Karfe uku na rana Aliyu yyi parkin dae dae kofar gidan kawu na lado kmr ynda yaji Ikram na kiransa, ya juya yana kallon Mami yace “nan ne gidan Mami” Mami tace “to Allah ya dora mu a kansu fita kayi masu sallama, Allah yasa ma yana nn” Aliyu ya fita ya karasa bakin kofar shiga gidan ya fara gyara Murya xae yi sallama sae ga yayar Shafa Hinde ta fito rike da bokitin wara xata talla, ya dan koma baya ita ko tana kallonsa cikin tsiwa tace “malam daga ina” yace “Amm nn ne gidan Kawu na Lado” Hinde tace “to ae babana ne,” yace “yana ciki” tace “eh” ya dan yi murmushi ganin ynda take amsa masa yace “to kice ana sallama da shi” ta juya ta koma cikin gidan, Baba shatu tace “kai yau ni naga shegiyar yarinya, uban me ya kuma dawowa dake Hinde, Allah idan wara ta tayi kwante yau sae kin cinye kin biyani kudi na don ubanki,” Hinde ta murguda mata baki tace “to wae ba ca aka yi ana sallama da baba a kofar gida ba”, Na lado dake xaune rike da radionsa yana cin barbajin awaran da Shatu ta dungure masa gabansa yace “in har ba kudi aka kawo min ba kije kice ma koma wanene ban nn, da me xan ji, da shegiyar talaucin nn ko da sallamar baki” yyi kwafa yaci gaba da cin warar sa, Hinde tace “wani mutumi ne fa yasa shadda me kyau da katuwar mota yaxo nemanka” ya mike tsaye da sauri har yana ball da kwanon gabansa yace “ni kuwa” Hinde tace “wllh” ba ko takalmi kafarsa yyi kofar gida da sauri, Aliyu na ganinsa ya dan dukar da kai yana gaishesa, Na lado da hankalinsa na kan jibgegiyar motar da yake gani kofar gidansa yace “yaro kayi batan hanya ne ko tambaya ka xo yi” Aliyu yace “A’a gun ka muka xo baba” ya fito da tulelen idonsa yace “to shigo yaro Allah dae yasa lfya” Aliyu yace “bani kadae bane ni da Mahaifiyata ce” kawu na lado ya xaro ido yace “a’a to ku shigo mana sannunku da xuwa” Aliyu ya bude ma Mami dake ta kallon Na lado daga cikin motar tana adduar Allah ya daurata a kansa, ta fito tana murmushi suka shiga gidan, Shatu ta mike daga gaban murhun da take da sauri tana gyara bakin xanin dake daure jikinta kmr na me sayar da kuli kuli tace “A’a baki muka yi malam” ko bin ta kanta Na lado bae yi ba ya shimfida masu wata bakar tabarma, Mami ta xauna tana murmushi, Aliyu kam kasa xama yyi da farar shaddarsa, Mami ta galla masa harara ba shiri ya xaune kan bakar tabarman yana kirkiran murmushi.
[2/25, 08:17] Zjy: ~Ikraam~ By Khaleesat Haiydar