Hausa NovelsIkraam Hausa Novel

Ikraam 12

Sponsored Links

~ By Khaleesat Haiydar 12…..
Washegari da Asuba Ammi ta sa Ikram tayi
shirin makaranta bayan sun yi sllh don Abba
yace shi xae dinga sauke ta a makaranta idan
xa shi gun aikinsa, idan an tashi kuma Ammi
taje ta daukota, tana saka uniform dinta
tace “Ammi ae safiya bae gama yi ba kina son
a sace ni ne a hanya,” Ammi ta galla mata
harara tace “ae da xan samu mai sace ki ma
ni da na huta” ikram ta xumburo baki ta
tsallake tean da Ammi ke hadawa taje dauko
safarta da takalmi a dakin Ammi, Ammi ta
daka mata tsawa “wae ke don ubanki wace
irin yarinya ce shi tean kike tsallakewa” kmr
xata yi kuka tace “to kin tare min hanyar” da
gudu ta dawo dakin bayan fitar ta tana cewa
“Ammi ni banga books dina cikin jakata ba”
Ammi tace “to kina ban ajiyar book ne” ta
fasa ihu tare da doka uban tsalle lkci daya
ta kwabar da tean gaban Ammi tana cewa
“wayyoo wllh ni baxan je ba Aunty xata min
duka” Ammi ta mike da sauri tana salati ita
ko tayi waje da gudu, Ammi ta bi ta ta
cafkota ta mammaketa snn ta hada ta da
biredin taci shi hka, shi dae Abba bae ce masu
komai ba, karfe bakwae saura suka fita gida
yana rike da Ikram da bata daina kukan
dukan da Ammi tayi mata ba, har cikin
makaranta ya shiga da ita snn yace da
malamar ko an tashi kar ta bari ta fita
mamarta xata xo daukarta, dariya malamar
tayi don su kansu Ikram ta ishesu a
makarantar. Ammi na kwashe taliyar da ta
dafa ma Ikram na rana kafin taje daukota a
sch, don ikram na son taliya ssae taji ana
sallama a bakin xaure, sae da ta gama xuba
taliyar a kula snn ta shiga da shi daki ta
dauko Hijabi, a tsakar gida ta hadu da kanin
Altine usman, tace “A’a usman daga ina, baka
je makarantar bane yau” yaron yace “mama
tace bani da lfya shi yasa ban je ba, wae
wasu mutane suka ce in ce suna sallama da
ke a waje” da mamaki Ammi tace “mutane
kuma, mata ne ko maxa” yaron yace “mama
guda biyu da mutumi guda daya ne” hankalin
Ammi ya tashi a xuciyarta tace shknn Ikram
ta kuma dauko mata magana kila, yaron ya
juya xae wuce Ammi tayi maxa tace “usman
an tashi daga makaranta ne, su Altine sun
dawo ne?” ya girgixa kai yace “A’a basu dawo
ba kuma ban ga yan makaranta na tafiya ba”
Ammi tace “to je kace masu gani nan xuwa”
yaron ya fita da gudu, Ammi tayi jigum a
tsakar gidan gabanta sae faduwa yake,
ganin bata ma masu jiran nata lkci take yasa
tayi kofar gidan, tsaye Mami take har lkcin
da wata mata da alamar kawarta ce, driver
na xaune cikin motar da suka xo da, Ammi na
ganinsu gabanta yyi mugun faduwa ganin irin
shigar da suka yi, ta dake tace “ina yinin mu”
Mami tayi murmushi tace “har ina tunanin ma
ko masu gidan basa ciki ne” Ammi tace “ina
ciki wllh” Mami tace “to sae dae kuma
maganar da ta kawo mu ba ta tsayuwa bace”
Ammi da gaba daya hankalinta baya jikinta
tace “to ku shigo mana” Mami tace “to
mungode” snn suka bi bayan Ammi suka shiga
gidan, Ammi ta shimfida masu tabarma tsakar
gidan suka xauna, snn ta dauko kujera yar
tsugunno ta xauna tana kallonsu tace “ina
fata dae lfya Hajiya” Mami tayi murmushi
tace “lfya qlau wllh, nima dae ina fatan da
maman Ikram muke mgana” gaban Ammi yace
dass, ta shiga uku maganarta ya tabbata knn
wani maganar kuma ikram ta dauko mata,
Mami ta katse mata tunaninta tace “kin yi
shiru kuma” Ammi tace “ehh ni ce, Allah yasa
ba wani abun tayi maku ba nasan ma baxae
wuce hka ba amma don Allah ku yi hkuri wllh
na gaji da yarinyar ban san ynda xan yi da
ita ba” dariya Mami tayi tace “ko daya wllh,
wata alfarma naxo kuyi min maman Ikram,
babanta na nn ne?” kai kawae Ammi ta sami
kanta da girgixa mata, mami tace “duk da
nasan baki san ni ba amma kisa a ranki ni din
musulma ce kmr ku kuma me tsoran Allah ce”
Ammi tayi shiru tana kallonta da mamaki, to
wace alfarma matar nn ke so daga gareta ita
da ba kowa ba, Mami ta katse mata tunanin
da take cikin nutsuwa tace “Ikram nake son
ku bani na rike don Allah ba don ni ba, kuma
nayi maku alkawari xan rike maku ita amana,
xan kuma bata tarbiyar da ya kamata snn
xata yi karatu ssae, wllh Allah ya dora min
son yara mata kuma sae gashi bae bani ba,
kuyi ma Allah da Annabi ku bani ita na rike
maku ita” tun da mami ta fara magana Ammi
ta saki baki tana kallonta.

Back to top button