Daudar Gora Book 1 Page 25
25_*
…….Turus Jasrah tayi ganin babu Abu Harith a inda ta barsa. Sai kuma ta nufi ɗakin barcinsa da tunanin koya shige. Nan ɗin ma dai babu alamarsa har cikin bathroom. Batare data kawo komai a ranta ba ta ɗan ɗage kafaɗa ta fito.
★Shi kuwa da tun bayan ficewarta ta ɗazun da kamar mintuna uku ya fice cikin ɓadda kama ya nufi sashen Miran Jasim. (Miran Jasim ɗane a wajen Ameera Banafsha, matar Tajwar Abdul-majeed ta biyu, shine ɗa na huɗu a wajensa, a maza kuma na biyu. Miran Arshaan ke bi masa. Sam babu jituwa tsakanin Ameera Banafsha da Malikat Haseena, ko mutuwar Miran Nayyar an dangantata da Ameera Banafsha a wancan lokacin. Sai dai da yake yaƙin sunkuru ne tsakanin matan biyu duniya bata san da haka ba. Burin Miran Jasim shine mulkar kujerar Shahan-shan tun yana ƙarami kamar yanda mahaifiyarsa ta horesa a kai, dan haka tayi matuƙar gwabza ɓoyayyen yaƙi akan marigayi Tajwar Haysam akan haihuwa har ALLAH ya bashi Tajwar Eshaan. Haihuwar Tajwar Eshaan wata ɗimuwace a nasararsu, saboda haka sun aikata abubuwa da yawan gaske na ganin bai kai ga matsayin da yake a yanzu ba ciki harda karkato da hankalin Miran Arshaan babban ɗa ga Ameera Aasfah amintacciya a wajen Malikat Haseena miji kuma ga Jasrah. Miran Arshaan sam bai biyo ƙyawawan halayen mahaifiyarsa ba, munafuki ne shima kuma yanada boyayyan nasa sirrin duk da riƙo irin na uwa da Malikat Haseena tai masa bayan rasuwar mahaifiyarsa, shiyyasa ya yarda ya haɗa kai da Miran Jasim domin kauda Tajwar Eshaan. Amma kaico UBANGIJI shi mai bawa wanda yaso ne, dan gashi dai Tajwar Eshaan ya zama Shahan-shan a daular ruman. Amma hakan baisa sun bar ƙulla-ƙulla na ganin cikar burinsu ba. ALLAH yasa kun gane).
Miran Jasim da dama tsumayen isowar Miran Arshaan ɗin yake ya miƙe daga zaman ƙasaitar da yay a katafaren falonsa da ya jiku da kayan more rayuwa. Juna suka tsirama ido cikin nazari dan bayan ƙullin tsakaninsu kowa nada ɓoyayyen sirri na akan ɗan uwansa. Miran Jasim ne ya fara kauda kansa ya maida hannayensa baya ya goya ya tako a sannu har tsakkiyar falon. Hakan yasa shima Miran Arshaan ɗin ƙarasa shiga suka tsaya gab da juna.
“Arshaan Akh Barka da isowa”.
Kai Miran Arshaan ya jinjina masa, sai kuma shima ya maida hannayensa ya goya a bayansa tare da ɗan takawa ya koma ta gefensa yana fiskantar window. Murmushi Miran Jasim yayi tare da juyowa yana kallonsa. Shima ya ɗan taka ya sake komawa gabansa. “Arshaan Akh kayi shiru, bayan kuma naga magana mai muhimmanci a cikin idanunka kamar yanda ka sanar dani ta waya”.
Huci Miran Arshaan ya furzar, sai kuma ya ɗago suna kallon juna shi da Miran Jasim ɗin. “Jasim Akh akwai damuwa ne. Yanzu nakeji wajen Zawjata. A ziyarar Yaron can ta yau wajen kakarsa akwai shirya ganawa tsakaninsa da yarinyar da shashashar matar can da ban san amfaninta garemu ba tasa muka aura masa”.
“What! Waye yay wannan ƙullin?”.
“Bana tunanin kana buƙatar tambaya dan kasan wace gadararriyar ce zata iya yanke wannan hukuncin. Na gaji da ganin matar can a raye.”
Murmushi Miran Jasim yayi da cije lips. Cikin ɗacin murya ya ce, “Ba Bushirat bace ta cancanci mutuwa. Waccan tsohuwar ce Arshaan Akh. Sai dai kuma su duka bazasu mutu yanzu ba”.
“To sai yaushe?”.
“Sai sunyi kuka akan gawar wancan shashashan yaron kamar yanda sukai kuka akan ta ubansa”.
Karan farko Miran Arshaan ya saki murmushi. Sai kuma ya warware hanunsa da ɗage kafaɗa. “Hakan ma shiri ne mai ƙayatarwa. Yaya batun uban yarinyar da ɗan uwanta? Dan sun sami Barrister Abdullah Aas a yanzu haka”.
Da sauri Miran Jasim ya kallesa. “Miyasa ban san wannan ba?”.
“Saboda bashi da muhimmanci dan na gama musu talala”.
“Arshaan kasan kuwa wanene Barrister Aas?”.
“Duk yanda saninsa zai iya bani tsoro ai bai kai razanin sanin muɗin su wanene ba a garesa nake ji?”.
“Ba ina maka magana bane akan ƙarfin iko”.
“Mi kake son na sani?”.
“Ba lokacin sanin tarihi bane. Kawai kayi duk yanda zakai na ganin ya dakata, su kuma a canja musu wajen zama”.
“Wai miyasa muke bukatarsu a raye?”.
“Saboda sune makamin da zamu juya yarinyar a ƙarƙashin ikon mu yanda muke so”.
“Kenan bamu da buƙatar matar hadimin can itama, dan ta gama mana aikinmu”.
“Matsalarta mai sauƙi ce. Daƙile Barrister Abdallah Aas ce mafi muhimmanci daga daren yau zuwa yinin gobe. Sai dai ina son a masa talala ta hanyar sanin inda suke kafin ya tsinta kansa a ramin damisa in har baiji gargaɗin farko ba”.
Miran Arshaan ya lumshe idanu da sakin siririyar dariya idonsa akan Miran Jasim. Shima dariyar yayi da masa jinjina…….
★… ★★…. ★….
A sashen Malikat Haseenah ma an gama shirya komai na tarbarsa, tun daga kan abincin da yake ci tare da kakar tasa har zuwa tsaftar sashen ma a yau ta kasance ta musamman duk da a kullum a tsaftace yake. An shirya kalolin abinci da ƙamshinsu tun duhun magrib ya cika ko’ina na sashen har maƙwafta ma na iya jiyowa. Abincine da Daneen Ammara ta girka sa da kanta saboda kar a cutar da shi ta hanyar girkawar, sai taimakon ƙanwar Malikat Haseenah da suke kira Yumma.
Gab da ƙofar fadar Malikat Haseena lafiyayyar motar da yake ciki ta tsaya, cikin rawar jiki ɗaya daga cikin Hadiman ya buɗe masa, sauran kuwa tuni sun zube ƙasa kan gwiyawunsu kawunansu a ƙasa domin girmamawa a garesa. Yaja fin mintuna biyu bai fito ba duk da an buɗe masa, sai da ya mula dan kansa sannan ya ziro ƙafarsa fara tas dake a cikin ƙyaƙyƙyawan blue ɗin takalmi mai tsananin taushi da ɗaukar ido da zai iya birge duk wani mai kallo, half cover irin na masu sarauta, kusan sakan biyar a tsakani sannan ya ƙara zuro ɗayar cike da ƙasaita. Tashin ƙamshin turarensa da takun sawayensa ya tabbatar ma Malikat Haseenah isowarsa. Da hannu taima dukkan amintattun hadimanta dake zagaye da ita nunin su fice. Har rige-rigen bin ƙofar da zata kaisu falon farko dazai fiddasu ta ainahin ƙofar sashen nata suke. A nutse tsohuwar ta ɗago idanunta ta sauke a ƙofar dai-dai shigowarsa. Tar-tar yake kallonta a cikin hasken ƙwan lantarkin daya haske falon kamar yanda itama take kallon ƙyakyawar fuskarsa dake a tsuke. Tai murmushi da jan numfashi ta fesar a hankali lokacin da yake isowa gabanta. Farin hannunta da fatar ta gama tattarewa saboda tsufa ya ɗan rissina ya kamo tare da kai tausasan lips ɗinsa ya sumbata.
“Amincin ALLAH da yardarsa su tabbata ga managarcin tushe mai cike da tsaftatacciyar yabanya”.
Idanunta ta lumshe a hankali da sakin murmushi a lokaci guda, sai kuma ta buɗesu tare da buɗe masa hannayenta. Rungumeta yay shima yana sakin ƙasaitaccen murmushi a karo na farko. Tsahon sakan talatin suna a haka kafin su saki juna ya dago amma bai ɗaga daga ranƙwafen ba. Hannunta ta ɗaura saman tausasashiyar sumarsa da a kallo guda zaka tabbatar da kuɗaɗen da take lashewa bazasu kasance na wasa ba.
“Aminci da yardar UBANGIJI ta kasance tare da kai kaima farar yabanya abin alfaharina”.
Idanunsa ya ɗan ƙankance da jinjina kansa yana murmushin da ita kawai ke iya ganinsa kai tsaye a fuskarsa kamar haka, sai ko Malikat Bushirat. Daga haka ya miƙe da ƙyau ya zauna ƙasan tattausar dardumar da aka shirya musu abinci, zama yay irin zaman sarakai da suka isa suka tumbatsa. Idanunsa ya zubama kakar tasa da murmushi ya gagara barin fuskarta, dan duk wannan ranar tanajinta rana ta musamman ne a gareta, sakamakon tuna mata da mijinta da ɗanta da takeyi da kuma tsananin ƙaunar jikan nata a yanzu.
“Nannah Kina lafiya?”.
“A zahiri dai lafiya nake, amma a baɗini cike nake da kewarka da ƙishirwar son ganinka a idaniyata Hafeedi”.
“Uhhm!” ya faɗa da ɗan lumshe idanunsa ya buɗe a lokaci guda. “To ki koma sashena mana, in har da gaske ne kina mun irin wannan buƙatar a kusa da ke”.
Yay maganar da yanayin zolaya, sai dai fuskar a kame take babu alamar hakan tattare da shi. Itama murmushi tai batare da tace komai ba dai-dai tana miƙa masa kofin data zuba madara.
“Kwana biyu mike faruwa da kai?”.
Yaja wasu sakanni kafin ya girgiza mata kansa alamar babu komai. Idanu ta cigaba da tsura masa har hakan ya ɗan sakashi tsarguwa ya kauda kansa gefe. Itama ɗauke natan tai gefe cikin rashin bama yanda yay ɗin muhimmanci. Sun kwashe kusan mintuna uku a yanayin shiru kafin shi ya katse hakan.
“Mamy fa?”.
Yay maganar a fisge tamkar yinta ya zama tilas ne a garesa.
Ita ɗin ma a ƙasaitancen ta bashi amsa da “Suna zuwa”.
Idanunsa masu girma da haske ya tsira mata. Kanta ta ɗauke gefe dan tasan kalmar (Suna zuwa) ɗin ce yake nemawa amsa.. Shima janye nasa idanun yay cike da basarwa da ƙasaitarsa ya ɗauka kofin data zuba masa madara……
A dai-dai nan Daneen Ammarah ta shigo da sallama hanunta riƙe dana Iffah dake cikin ƙyaƙyƙyawar doguwar rigar abaya baƙa datai matuƙar amsar jikinta, Shirine na musamman da Daneen Ammarah ta zauna domin yinsa gareta da kanta. Cikin ƙanƙanin lokaci sirrintaccen ƙamshin jikinta ya shiga rige-rigen isa hancin Malikat Haseena da mai gayya mai aiki. Shaƙar ƙamshin turaren da zaton Daneen Ammarah ce kawai mai shigowar ya sashi ɗago idanunsa, cikin Sa’a kuwa ya sauke su a kanta. Murmushi Daneen Ammarah da suka haɗa ido ta sakar masa, yayinda shi kuma fuskarsa ke nuna tsananin ƙaunar da yake mata a zahiri.
Haka itama Malikat Haseena murmushi ne ƙawace a fuskarta idonta akan Iffah da kanta ke rissine taƙi kallon komai. Ƙara riƙe hanun Iffah Daneen Ammarah tai da ƙyau kamar za’a ƙwace mata suka cigaba da takowa a nutse. Malikat Haseena taima Daneen Ammarah nuni ta zaunar da Iffah a kusa da ita, sai ya zam suna facing juna da Tajwar Eshaan, sannan kuma a tsakkiyar su shi da Malikat Haseena ɗin..
Gaba ɗaya ya tattara hankalinsa ga Daneen Ammarah tamkar baiga tana tare da wata ba, “Amincin ALLAH da rahamarsa su tabbata ga Mamy na!”. Ya faɗa akan laɓɓansa kamar bashi yay maganar ba, dan ko Iffah da Malikat Haseena ba jinsa sukai ba sai ita Daneen Ammarah da takai zaune kusa da shi. itama ta sake sakin murmushi da kaɗa masa kanta. “Tare da kai Abni, Amincin ALLAH da rahama da kariyarsa su tabbata a gareka. Ina fatan kana cikin ƙoshin lafiya da nutsuwar zuciya?”.
Kansa kawai ya kaɗa mata, sai kuma ya ɗan ɓata fuska. Murmushi ta sake saki da maida idanunta kan Iffah da Malikat Haseena kema magana.
“Hafed-ti! An hanaki barci ko?”.
A hankali Iffah da ƙirjinta ke faman harbawa da sauri-sauri ta girgizama Malikat Haseena da tai maganar kanta. Cikin sanyin murya da sauƙaƙa fitar sautinta ta ce, “A’a Mamma ai bamma kwanta ba”.
“Masha ALLAH yaya jikin naki?”.
“Alhamdulillahi Mamma, Aminci ALLAH ya tabbata a gareki a wannan lokaci”.
“Amin. tare dake kema Negar”.
Iffah ta ɗan murmusa har yanzu kanta a rissine. Daneen Ammarah dake kallonsu da murmushi ta janye idanunta ta maida ga Shahan-shan daya sake ɗauke kansa tamkar bai san mike faruwa ba ma.
“Ibnati!”.
Ta kira sunan Iffah a tausashe kamar yanda ta saba.
“Na’am Mamy”.
Itama ta amsa mata kamar yanda ta saba. Sai dai ta kasa iya ɗago kanta, dan duk da bata san wanene ba gaba ɗaya kwarjininsa ya cika falon har tanajinta a matuƙar matse kamar ta tsilla da gudu kozata samu nutsuwa….
“Ga yaro na”.
Ta faɗa cikin sigar son ɓiye mata ainahin wanene ɗin. Iffah da bata damu da son sanin gaskiyar zancen Daneen Ammarah ɗin ba ta amsa da alamar raunin murya a tare da ita. “Amincin ALLAH ya tabbata a gareka. Barka da wannan lokaci”.
Shiru babu alamar zai amsa mata, ran Iffah ya sosu dan a rayuwa ta mugun tsanar wulaƙanci, duk yanda taso ta danne sai ta kasa, a karan farko tun shigowarsu falon ta ɗago idanu cike da jin zafi, dai-dai ya ɗan ɗago shima zai kai kofin madara bakinsa idanunsu suka rufta cikin na juna…
Zabura Iffah tayi da ware manyan idanunta, yayinda shima yay ɗan tsai yana kallonta na sakanin da basu gaza biyar ba, sai kuma ya janye abinsa cikin halin ko’in kula ko fahimtar yanayin data shiga ya sake gyara zaman ƙasaitarsa…….✍️
*LITATTAFAN DAI SUNE KAMAR HAKA*
*DAUDAR GORA Billyn abdul*
*KI KULANI hafsat xoxo*
*A RUBUCE TAKE Huguma*
*RUMBUN K’AYA Hafsat rano*
*IDON NERA Mamuh ghee*
_LITTAFI DAYA: 400_
_LITTAFI BIYU: 600_
_LITTAFI UKU: 800_
_LITTAFI HUDU :1000_
_LITTAFI BIYAR: 1200_
_KUDIN TALLATA MAKU HAJOJIN KU KUWA SUN KASHI KASO 4:_
_TALLA A DUKKANIN SHAFUKAN MU DA KE MANHAJAR YOUTUBE, FACEBOOK, TELEGRAM, WATTPAD, INSTAGRAM, WHATSAPP GROUPS DA STATUSES. YA KAMA :25,000(DUBU ASHIRIN DA BIYAR)_
_TALLA NA IYA SAMAN SHAFI DAYA NA BOOK DAYA: 1000 1K_
_TALLAN TSAKIYAR SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA: YA KAMA 800_
_TALLAN KARSHEN SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA. YA KAMA NERA 500_
_ZAFAFA BIYAR 2023!! ZAFAFA PAID BOOKS!! LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_
ZAKU TURA KUDIN A WANNAN ACCOUNT DIN ME DAUKE DA SUNAN
MARYAM SANI
ACCESS BANK
0022419171
SAI A TURA SHAIDAR BIYAN
09033181070
IDAN KUMA KATI NE KU TURA TA WANNAN NUMBER HADE DA SHAIDA
09166221261
*ƳAN ƘASAR NIGER. ZAKU TURA KATIN AIRTEL TA WANNAN NUMBER WAYAR KAI TSAYE KUMA*
+227 90165991
Books biyar 1250CFA
Books hudu 1050CFA
Books uku 850CFA
Books biyu 650CFA
Bookk daya 450CFA
KARKU BARI AYI BABU KU, KU GARZAYO MU DAMA A CIKIN WADANNAN GWALA-GWALAN LABARAN MASU MATUKAR SANYA NISHADI.
MUNGODE DA ZABIN ZAFAFA BIYAR A KOWANNE LOKACI.
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*
✨Ɗ ✨
( )