Adandi 22
22*
Kallonta Dad yayi yayi murmushi yace “meyasa kikace na aure ta pretty?” Kawar dakai tayi tace “saboda ta cikemin gurbin da mamy na ta kasa cikemin Dad ina buqatar uwar da zata dauki lamarina da muhimmanci duk da nasan baa taba sakewa tuwo suna Mamy itace mahaifiyata amma zan samu kulawa ta wasu bangarorin” mikewa yayi ya ruqo hanunta yace “zan duba yuwuwar hakan Pretty farin cikinki nafi buqata fiye da komai tayi murmushi daidai lkcn da Aunty Hasina ta shigo da kayan abinci ta ajiye tace “yadai naga kun miqe Samha badai har tafiyar ba” ajiyar zuciya tayi tace “na gde da kulawarki gareni kece mutum ta biyu da bazan taba mantawa dake ba Aunty” murmushi tayi ta janyota jikinta wasu hawaye suka zubo mata tace “inajinki kamar yata ta cikina Samha koda kin tafi kada ki manta dani don Allah ki daukeni uwa a gareki kinji” ta juya ta kalli Alh Sa’ad tace “Alh zaka daukemin yata bazanso hakaba saidai dan babu yanda zanyi kaine me iko akan komai” sukayi dariya dukkansu sannan sukaci abincin Samha tana bawa babanta abincin a baki shima yana fata soyayyar tsakanin uban da yarsa tayi mugun burge Dr Hasina taji dama ahlinta ne haka.
Bayan sun gama cin abincin Dr Hasina da Rahmah suka rakasu tsohon gdan Samha suka debi kayanta sannan sukayi sallama suka tafi ita kuwa Rahmah tayi uwa Dr Hasina cewa tayi bazata zauna anan ita kadai ba dole sai gdanta ta koma.
Sai dare sosai suka shiga Abuja dake tafiyar mota ce suna zuwa Samha ta tarar gdan babu kowa wai Mamy ta tafi Maiduguri yar yayarta ta haihu dakinta ta shige tayi kwanciyarta duk sanda ta tuna yanzu itafa ba budurwa bace sai tayi kuka kamar ranta zai fita ta qara jawa Abdul Allah ya isa.
Haka kwanaki sukayita tafiya saida Mamy tayi sati ta dawo lkcn Samha ta qara warwarewa cima me kyau ga kulawar mahaifinta har tayi qiba tayi shar da ita babu abinda takeyi saidai tayi wanka taci abinci tayi sallah a cikin kwanakin ne Dr Mus’ab ya kirata sau daya yake fada mata zaizo zasuyi wata mgn akan shirye²n bikinsu tunda Dad ya yarda an sauko dashi yanzu haka bikin saura sati uku lkcn da yazo ta jima a daki a kwance kafin tayi qarfin halin miqewa ta fito a garden suka zauna suka gaisa tun daga yanayinta ya fahimci akwai damuwa a tattare da ita ya kalleta sosai yace.
“Nazo da tawa damuwar kuma sai na fahimci kamar taki tafi tawa Samha meye yake faruwa ne kusan sati hudu kenan banajinki a yanayin dana saba jinki kin daina sakin jiki dani kin daina bani kulawa sai na kiraki sau uku baki dagaba meyene?” Hawayen da take boyewa ne suka gangaro mata tace “bansan wanne kallo zakayimin ba idan na fada maka ainihin abinda ya faru Mus’ab rayuwata taqi tafiya kamar yanda ta kowa take tafiya Mus’ab Abdul yayimin tabon da bazai taba gogewa a zuciyata ba na tsaneshi Mus’ab na tsani Abdul wlh na tsane don Allah Mus’ab ka janyewa aurena” dagowa yayi ya kalleta da sauri yace “kamar ya na janyewa auranki Samha?” Cikin kuka tace “ina nufin ka hqr dani kace da Dad ka fasa aurena wlh nafi buqatar rayuwa ni kadai bansan irin kallon da zakayimin ba duk ranar daka fahimci nidin ba budurwa bace wani ya lalata min budurcina ta hanyar zalumci Mus’ab don Allah kace ka fasa…” Rufe mata baki yayi memakon taga alamun bacin rai ko damuwa a tattare dashi sai taga yayi murmushi yace “abinda yasa kike qara burgeni kenan Samha qarya bata cikin tsarinki wlh tun washegarin ranar da abin ya faru aka turomin saqo da wata number da yake nunamin abinda ya faru dake a ranar saida nazo Katsina haka na gama bulayi na ban samu ganinki sai bayan na gaji na koma na kama hotel ina hutawa sannan saqo ya kuma shigowa wayata akace min dama kayi hqr Samha tayi maka nisa Samha a cikin saqon har gargadina akayi cewa kada na kuskura nace zan aureki ke matar Yariman Katsina ce sannan aka qara tabbatar min cewa harma cikinsa gareki kuma yanason kayansa nayi qoqarin bayyanawa Dad wannan saqon sai kuma naga rashin dacewar hakan saboda ya kamata ace ya zama sirrin mu saboda mune zamu rayu tare kodan rufuwar asirin yayanmu amma wani abu nima da yake damuna har yasa na sauko da aurannan namu Samha Hajiyata tace saidai na aureku ku biyu keda yar qawarta bama wannan ba Samha abu daya dana boye miki shine inada mata da yarana biyu….”
Dagowa tayi da sauri cikin tsananin mamaki tace “kana da Mata harda yara biyu amma Sir baka taba fadamin ba meyasa ka boyemin hakan…” Saurin katseta yayi da cewa “aa ba haka bane lkcn dana fara neman auranki banida mata mun rabu da ita so wata uku kenan data dawo gdana itama Hajiya ce tasa na dawo da ita wai a cewarta dana auro mata ke da muka hadu ADANDI gara na da Maryam matar data nemi kasheni kawai saboda taga hotonki a wayata”…..
_Kuyi hqr da wannan sisters_
*UMMUH HAIRAN CE…✍*
[2/13, 8:26 PM] UMMUH HAIRAN CE…✍: *_AD_*
*_Dont read this book if you are not married. Mature content contained in it. Reader discretion is advised. You read at your own risk._*