Yar Zaman Wanka 15
A wurin Inna ta baro su ta dawo gida riƙe da ledar, tana shigowa ta ajiye ledar ta nufi kujerar da Abdallah ya zauna ta danna da hannunta, ta ƙara taɓa inda matarsa ma ta zauna ta taɓe baki ta ce.
“Halima kin ga abin da nake faɗa miki ko? Da kin ce mutanen nan su zauna a ƙasa dan wallahi baki ji yadda kujerar ta faɗa ba gabaɗaya ta lotse dan ji na yi har katako da ƙarfen ciki ina taɓowa musamman wacce Sojojo ya zauna, dai dai ma an yi ba bashi sun kawo kaya masu tsadar gaske” Ta faɗa tana taɓe baki ta zauna a ƙasa ta shiga fito da kayan jariran na cikin ledar kaya ne masu kyau da tsada har da turmin atamfa.
“Kai, kai, kai, taɓɗi ashe dai Sojojo an iya abin arziƙi, to Allah amfana” Har lokacin Sadiya bata ce mata komai ba dan ita yanzu abin Inna yana ɗaure mata kai sosai ta gaji ma da wannan ZAMAN WANKAN gabaki ɗaya.
“Yo ko ki yi magana ko ki ƙyale, duk ɗaya dan kin ga wannan kayan da suka lodo miki kamar bashi yake dan kin ga matarsa ma tsohon ciki gareta dole idan ta haihu ke ma ki ki mata” A dai dai nan Imran da ransa ke ɓace ya shigo da sallama ciki-ciki.Amsa masa Sadiya ta yi.
“Imirana ka ga abin arziƙin da Sojojo ya kawo maka, kaima dai Imirana wallahi da karambani kake, banda karambanin akuya mai sa ta leƙa ɗakin kura, ina kai ina wannan mutumin him guda dashi, yanzu a ce ka rasa aboki sai wannan rungujejen abu kamar himilin kaya ina abokin ka Abida tun ranar da ya kawo mu shiru kake ji wai malam ya ci shirwa, amma wannan Sojojon da kuka jeru sai na gan ka abu ɗul kamar ruwan aski.
Banza ya mata ya shige bedroom dan daga Inna har Sadiyar ma haushinsu yake ji.
“Aniyarka ta bika Imirana in ƴaƴan naka kake yiwa baƙinciki dan an kawo musu kaya, wato so ka yi kuɗi ya bayar ka yi wuf da su ko?, gashi ma har yau babu sadakin gado babu dalilinsa, ka murtsuke ƴar mutane ka mata ciki ta haifa maka ƴaƴa har biyu amma har yau babu ragunan suna ga lokaci na ta tafiya, sai dai ka kawo wani ɗan nama a ƴar baƙar leda wai na me jego ne, yo wane irin me jego kawai a kawo tirkakkun raguna, ah to mun gaji da gafara sa bamu ga ƙaho ba, dan ba dani ba gaɗa a kabari in ji ƴan magana”
Babu wanda ya ce komai shi ya shige ɗaki ya kwanta yana ta jiyo Inna yana kuma tunanin abin da zai mata.
“Oh ni Ashrofa sai ka ce an aiki bawa garinsu, daga cewa za ta je gidan su ƙawarta ta dawo amma har yanzu bata dawo ba”
“Me za ta miki to idan ta dawo ɗin?”
“Haba Halima har na rasa abin da za ta min yunwa nake ji”
“To ki zubo abincin mana”
“A’a ni ba shinkafa zan ci ba so nake ta dawo ta dafa mini indo momi (indomie) Taliyar yara akwai daɗi wallahi”
Kallonta kawai Sadiya ta yi bata ce komai ba.
~DARE~
Tun da ya kwanta yake juyi a katifar, ji yake kamar ya je ya iyo waje da Inna daga ɗakin nan ya kulle, dan gabaɗaya yau ba ya jin jikinsa dai dai. Zaune yake ya zabga uban tagumi mararsa sai murɗa masa take tana neman ɗauki, haka ya dafe marar yana yin salatin annabi S.A.W Ya daɗe a haka zuwa can ya tashi ya leƙa bedroom ɗin fitilar a kashe sai dai ɗakin ba duhu sosai da yake hasken farin wata ya ɗan shigo ta gefen labule. Ba ka jin komai sai ƙaran komai a ɗakin dan Inna ko munsharin ma bata yi, hakan ya sanya ya ɗan fara lalume har ya ƙarasa wajen gadon tsaye yake yana ta nazari so yake ya gano wacce ce Inna wacce ce Sadiya dan ya lura yanzu kowacce tana iya ɗaukan bargon kowacce ta rufa haka zalika suna iya canjin wurin kwanciya saɓanin da kowacce na kwanciya a gefen da take kwanciya.Kan gadon ya hau sai da ya zauna a tsakaninsu ɗare-ɗare so yake ya gane matarsa ya shiga bargonta ya kwanta a kusa da ita ko ya samarwa kansa nutsuwa, kunne ya kai ya kara a saitin bargunan dan ya tantance na Sadiya dan gabaɗaya kowacce ta rufa ne har kanta.
Kunne ya miƙa jikin bargon Sadiya dan ya tantance ita ɗince a ciki ko kuma Inna ce a ciki. Garin kara kunne sai ya ɗan zame hannunsa ya buge na cikin bargon ashe dai Inna ce a ciki, wani uban juyi da ta yi da miƙa shi ya sanya Imran tsorata dan ya ɗauka zaune za ta tashi, idan kuwa ta gan shi a kan gadon a tsakiyarsu tabbas za a kwashi daru, da sauri ya yi wata shala sai gashi a gefen gadon wurin inda akwatuna suke, durƙusawa ya yi yana kiran sunayen Allah. Jin shiru babu motsinta sai ya ɗago kai a hankali ganin ta cigaba da barcinta sai ya lallaɓa ya fito daga ɗakin da rarrafe dan ba ya so ma ya tashi tsaye ta ji motsinsa a samu matsala.
Haka ya dawo falon wani haushi da takaici na damunsa, ga mararsa da har lokacin bata daina ciwo ba, fitilar falon ya kunna ya fita domin zuwa kicin.
“Kai da matarka halalinka amma kake raɓewa in za ka wajenta kamar wani kwarto” Cewar Imran a zuciyarsa, yana nufar kicin ya ɗakko jar kanwa ya jiƙa ya sha dan ya rage sha’awar da ke damunsa haka ya dawo ya kwanta yana jin ɓacin rai fal ransa, ya so ya shiryawa Inna wani abun cikin daren nan amma rashin nutsuwa da kuzari ba za su barshi ba haka ya haƙura ya kwanta yana cewa “In kere na yawo zabo na yawo wata rana za a haɗu.
*WASHE GARI*
Kamar kullum yau ma haka Inna ta haɗa ruwa sai dai cikin ikon Allah har ta wanki Hassan ta gama amma bai sawaya ba, haka ta shirya su tsaf.
*DA YAMMA*
Suna zaune a falo Ashrof, Sadiya da kuma Inna Imran ya fita ba ya nan, sallama ake yi a Ashrof ta amsa da ta leƙa sai ta ga Abid ne.
“Ya Abid ina wuni” Lafiya ƙalaw Ashrof ya mama ina Hajiya Inna?”
“Mama tana gida Inna kuma tana ciki in nemanta kake”
“Kamar kuwa kin sani saboda ita na zo, ki ce tana nan ana shan ZAMAN WANKA”
“Eh” Cewar Ashrof tana ƴar dariya.
Tare suka shigo Inna na ganin Abid ta fara murna tana cewa
“Lale da Abida sannu da zuwa”
Shi ma dariyar ya yi ya zauna yana gaishe da Inna suka gaisa da Sadiyar.Ya tambayi kwanan yaran nan aka bashi amsa da lafiya ƙalaw.
“Wallahi abubuwa ne suka ɗan sha kaina ban samu na dawo ba, na ga yaran ba”
“To wane gani kuma kai da muka dawo da kai daga asibiti da su” Cewar Sadiya tana ɗan murmushi.
“Haba Sadiya ke me yasa kike haka ne ni wai, ai in kin ji an ce za a ga mutum ba wai gani na ido ba ake nufi. Baki ga ƴan siyasa ba ko masu kuɗi idan ƴan maula suka je wurinsu sai su ce zan ganka zuwa gobe, to ai suna nufin za su sallami mutum da wani abun shi ne hausar” Cewar Inna tana kallon Sadiya, Sadiya kwa da Ashrof kunya ce ta rufe su ai hakan kamar roƙo ne. Wani yatsina fuska Sadiya ta yi take yiwa Inna kallon irin me yasa haka.
“Kai ka ji ni da mata, yo sai ka ce wani wanda na yi saɓo, kawai dan yarinta ta sa kun kasa gane inda maganar Abida ta dosa na warware muku zare da abawa sai ki rinƙa zare min ido kamar dai ke ce uwata mai daddawa”
“Rabu da ita Inna ai gaskiya kika faɗa kuma ni ma dama irin ganin da na zo na musu kenan” Cewar Abid yana dariyar maganganun Inna sosai ya so ya dawo amm abubuwa suka masa yawa amma da tuni ya dawo ko dan ya ci dariya.Ya kuma ga irin zaman da ake tsakaninta da abokin nasa dan Imran ya ƙi bashi labarin komai kuma ya san tabbas akwai wata a ƙasa dan babu yadda za a yi a zauna lafiya tsakanin Imran da Inna.
“Ga wannan Inna naki ne wannan kuma na jarirai” Ya faɗa yana miƙa mata manyan ledoji guda biyu, ɗaya kayan jarirai ne da less mai shegen kyau na Sadiya, sai kuma ɗayar atamfa ce da goron cikin farar leda.
“Ayyiriri, taɓɗi yau ake yinta ai shi sa jiya nake tambayarka a wajen Imirana , nagode Allah saka da alkairi, ya buɗa maka, wallahi Abida ka fiye min Imirana sau dubu ka ga Imirana ko goron murtala (Ashirin) Bai taɓa siyo wa ya kawo min ba bare turmin zane” Cewar Inna tana sakin goɗa tana ɗaɗɗaga atamfar.
“La ba komai Inna in ba a kyautatawa tsofaffi ba wa za a yiwa”
“Kai dai da ka san hakan amma Imirana mai ya sani yaron nan banda ƙafafa da nuna shi mai gida ne”
“Imran ko Inna”
“Shi mana, bari ma na baka labarinsa, amma sai na fara baka daga farko ranar da na kwana ban yi bacci ba”
“Baki yi bacci ba fa Inna, garin yaya?”
“Wallahi fa Abida, haka kawai ban ji ba ban gani ba,ina ranar da ka kawo mu daga asibiti har nake baka labarin abokin Imirana wanda ke wasarere da jikinsa”
“Eh Inna na tuna”
“To wallahi a ranar nan ni na san irin kwanan da na yi a gidan nan” Ta faɗa tana share ƙwallah.
“Subhanallahi Inna ba dai a waje kika kwana ba da sanyin nan?”
“Haba Abida ana ga yaƙi kana ga ƙura yo ba gwara a saka ni a randa ba in kwana da irin kwanan da na yi ranar nan kai ni dai sai da na ji ina ma ban taho ZAMAN WANKAN nan ba, ni da na kwana a tsakanin katako sama katako ya tokare ƙasana katako ”
“Katako kuma Inna”
“Yo a ƙarƙashin gado fa na kwana, bayan nna nawa da gado ya matse yadda ka san an yiwa mota lodin shanu haka na ji, wallahi ba dan na shafa man zafi ba da Allah kaɗai ya san me zai faru.
” Ta faɗa tana ɓantarar goron da fa ɗauka daga cikin wanda aka kawo mata ta ƙulle ledar.
“Garin yaya?”
Shiru ta ɗan yi dan bata son faɗar gaskiyar dalilin da ya sa ta kwana a ƙasan gado dan har yau bata daina jin tsoron aljanin ba kuma har yau tana ganin kamar dai yana kallonta a gidan.
“Sanyin garin nan ya sa na kwana a ƙasan gado” Ta faɗa tana ƙara gutsurar goro fuskarta ɗauke da damuwa.
“Sanyi fa Inna, lallai sanyi bai kyauta ba” Ya faɗa yana dariya dan ya fuskanci bata faɗi gaskiyar abin da ya sa ta kwana a ƙasan gadon ba dan daga yadda ta faɗa ya san ta faɗa ne kawai, ga kuma
yadda take bada labarin ma kaɗai abin dariya ne.
“Sanyi mana, ai ba fa shi ne abin da na fuskanta ba kaɗai, ka san Hassan ya zo da baiwa a jikinsa wato haka kawai sai yaro ya ringa saɓaɓa-saɓa ya bar ainihin halittarsa ya koma ta miciji”
“Miciji Inna” Ya faɗa da yana son tabbatarwa dan ya san dai Imran ya xe fatar bayan yaron ta miciji ce.
“Miciji mana, ai a washe gari da haihuwarsa ya koma miciji da kan mutum amma saboda rashin imani na Imirana haka ya garƙameni da micijin nan a ɗaki tun ina neman ɗauki har na gaji, ya sanya na rinƙa karanta alif an baki waw zal, kai daga ƙarshe dai sai ga Azumi a saman drower na hau can tsililiko ina reto”
Dariya kawai yake, da jin labarin ya san dama tabbas a rina wai an saci zanin mahaukaciya dan ba za a ƙarƙe ƙalaw ba da Inna da Imran saboda basa jituwa.