Yar Zaman Wanka 12
1️⃣2️⃣
WASHE GARI
Bayan Inna ta yi sallah ta fita duk da jikinta babu ƙwari, ta hura wuta ta ɗora ruwa, dan Sadiya cewa ta yi ta barta ta ɗora amma Inna ta ƙi dan a cewarta Sadiya ɗanyen jiki gareta na jego, shi kuma jikin jego bai son garaje haka dai ta rinƙa komawa tana iza wutar har ruwan ya tafasa. Bayan ta yiwa Sadiya wanka ta barta a bayin ta fito, haka ta haɗa ruwan wankan yaran amma da ta zo maimakon ta shiga can cikin bedroom sai ta ajiye a falo, haka ta kwaso komai da za ta buƙata ta dawo ta ajiye a falon. Husaini ta fara janyo gadonsa ta ajiye ta koma ta janyo na Hasan tana jan sunayen Allah a ranta. Imran da ke zaune yana kallonta ganin tana shirin tuɓe Husaini ya ce.
“Inna wai kina nufin a falo za ki wanki yaran nan? Bakya jin yadda ake sanyi ai cikin ɗakin ya fi ɗumi”
Banza ta masa ta cigaba da cirewa Husaini famfas, sai da ta gama tana shirin tsundum yaron a ruwa Imran ya sake mata magana a karo na biyu.
“Haba Inna ai da tausayi fa ace kin wankesu a falo baki ji har iska shigowa take ba”
Dakatawa Inna ta yi daga ƙoƙarin saka Husaini a ruwan ta kalli Imran a shelaƙe tana yatsina fuska ta ce.
“Wai ni kai ka ji na shiga harkar ka ne a yau? Ko baka san idan mutum ba ya ta taka ba ka rabu da shi ba” Ta faɗa tana harararsa dan tun da ta zargeshi da zuba mata abin da ya ɓata mata ciki sai take jin mugun haushinsa saboda irin yadda ta yi ta sawu bayi.
“Yau kuma Inna ke ce bakya son magana?”
“Kai ka kiyaye ni, na faɗa ba na son maganar, kuma da kake zancen wankan yara a falo to ina sane wai karuwa ta taka matar aure, a nan na yi niyyar zan musu wanka” Ta faɗa tana sanya Husaini a ruwan ta shiga yi masa wankan. Shi dai Imran bai sake magana ba ganin ta wani haƙiƙice tana magana. Sai da ta gamawa Husaini ta shirya shi tsaf ta kwantar da shi dan tun tana shafa masa mai bacci ya ɗauke shi.
“Bismillahir rahmanir rahim, li’ila fi ƙuraishin, aniyar kowa ta bishi, iyyaka na’abudu wa iyyaka nasta’in” Cewar Inna lokacin da ta miƙa hannu za ta ɗauki Hassan.
“Ana tsoronka ɗan mayya, ya ce daga ni har uwata” Imran ya faɗi karin maganar yana kallon Inna.
“Tsoro wajibi ne ai,har gwara wata wainar da ta wake, wani da ya laɓe jikin bango dan tsoro har da sakin fitsarin wahala” Cewar Inna tana cirewa Hassan kaya amma kuma gabanta n dukan uku-uku. Jin maganar da Inna ta faɗa Imran ya ɓata rai dan sai ta tuno masa da jiyan a ransa ya ce
“Fitsari ai ba ni kaɗai ba ke da kika yi arba da aljani kike saki fitsari a tsaye tafiya ma gagararki ta yi sai da rarrafe kika shige ɗaki, har da kwanan ƙasan gado” A fili kuma ya ce.
“Ki yi ki wankeshi dai kafin ya sawaya, dan yana fara sawaya zan fice in garƙameki a falon irin na jiya”
Muƙut Inna ta haɗiye wani yawu da bata san lokacin da ya taru a bakinta ba, jin abin da Imran ya ce na sawayar Hassan, kallon yaronkawai take tana ƙiyasta yadda za ta yi wurgi da shi idan ya zama miciji a hannunta.
“Dan Allah Imirana ka sassauta muryarka kar fa yaron nan ya ji ka tuna masa ya sawaya, ni fa dama saboda gudun sawayar tasa na ƙi zama a cikin ɗaki na fito falo dan idan na ga ya ɗakko sawaya in bar maka shi in gudu” Cewar Inna cikin sanyin murya.
Dariya ya ƙyalƙyale da ita ya kalli Inna ya ce.
“Wai dama dibara ce kika yi Inna, taɓɗi lallai kuwa kin kama riɓaɓɓiyar igiya dan babu abin da zai hana ni gudu, miciji fa”
Inna Kallon Hassan take da yake wani miƙa hannunsa yana wani markwaɗewa ta ce.
“Haba Hasanunu daure-daure ka maida baiwarka ka ji ɗan albarka, idan na wanke ka, na gama shiryaka sannan uwaka Halima ta fito daga wanka sai ka sawaya in ma mesa za ka koma wato babban miciji sai ka koma, amma wallahi jiya ma ban ji daɗin karon ba tun da ka sawaya na rinƙa tsuma ga ubanka Imirana ya kulle ni a ɗakin ai ka sani dan kana ciki kaima har saman drower kaya na ɗane sai gani a ka ɗare-ɗare ba ka ganni ba lokacin ai mun haɗa ido da kai da ina saman ko?” Inna ta kai ƙarshen maganar tana rausaya kai kamar ƙadangaruwa, ta faɗa da alamar tambaya kamar dai yaron ya ma san me take cewa.
” To ka yi haƙuri ka ji, Inna Azumi ce matar Malam wallahi ZAMAN WANKA na zo wa uwarku Halima ka ga ai baƙon ka annabinka, ni da za ka bi ta tawa ma da ka tsaya a mutum ɗinka har na gama ZAMAN WANKANA na tafi in yaso idan na bar muku gidanku idan ka sawaya ka koma miciji kar ka dawo mutum sai ka yi sati guda ko ma wata guda iyayenka su yi ta famar tsere da kwanan zaune dan nasan dai ba wanda zai haɗa ɗaki da miciji ya yarda ya runtsa dan tsoro ba zai barshi ya yi ko da gyangyaɗi ba bare a kai ga bacci”
“Haba Inna wannan wace irin kuɗuba ce kike yiwa yaron nan?” Imran da bai san yadda aka yi ba ya miƙe tsaye sai ganinsa ya yi tsaye cankarkar a tsaye.
“Yo ba dole ba in masa kuɗuba ya bari sai na tafi saboda babu daɗi ni tsohuwa ina ganin tashin hankali muraran amma ku da yake da ƙwarinku kuma da sauranku, sannan ma ku kuka haifesa sai ku yi rayuwarku da shi a micijin”
“Dan Allah Inna ki bar wannan maganar ki wankeshi kawai”
“To” Ta ce rana tsunduma Hassan cikin ruwa tare da karanto fatiha da salatul fati”
Ganin ta sanya Hassan ɗin a ruwa sai hankalin Imran ya ɗan kwanta ya koma mazauninsa ya zauna yana haɗiye wani yawu muƙut.
Ta gama wanke wa Hassan kansa zuwa fuska ta ɗauraye tana cikin saɓa masa jikin, Imran sai kallonsu yake gabansa na faɗuwa dan shi ko kaɗan bai cire rai daga cewar Hassan ɗin ba zai koma miciji ba, ji yake kamar ya tashi ya fice amma kuma ba ya so Inna ta zargi wani abu haka dai ya daure ya zauna ba dan ya so ba.
A ɓangaren Inna ma haka abin yake wankan take masa amma kamar wanda ta riƙe wuta, tana wanke yaron ne dan dai ba yadda za ta yi, a haka ta juya bayan yaron inda yake fatar miciji ta shiga wankewa cikin tsoro dan gani take tamakar miciji take yiwa wanka, tana ta saƙawa a ranta cewar in ba lalura ba babu yadda za a yi ta haɗa hanya da yaron nan ba bare kuma har ta wankesa. Juyo cikin yaron da Inna ta yi sai gani ta yi ya koma kamar fatar bayan, idanu ta zaro har tana ɗauke numfashinta dan ta lura Hassan ya fara sawaya. Dakatawa ta yi da wankan ta ajiye sosan.
Imran da ya lura da yanayin Inna ya sauya amma dai bai san dalili ba dan bai ga abin da ta gani ba ya ce.
“Inna cigaba da masa wankan mana na ga kin ajiye soson kuma baki ɗauraye masa jikin ba kin bar masa duk kumfa” Ya faɗa kamar wanda ke jira a ce masa kulle ya ce cass dan gabaɗaya a tsorace yake.
Shiru dai Inna bata tanka masa ba, tana ganin ikon Allah kawai tana jin kamar ta saki kuka ta yi ta ƙugawa jama’a su kawo mata ɗauki in ba ƙaddara ba ace tana riƙe da miciji, halittar da cikin mintu kaɗan za ta sareka ta yi ajalinka lokaci guda.
Gabaɗaya jikin Hassan ɗin ya fara sawaya, Imran da ya lura da hakan ya ƙame a zaune tamkar soja, gabaɗaya ya tsorata da lamarin yaron dama da ace ba ɗansa bane babu dalilin da zai sa ko hanyar da yaron yake ya bi amma kuma addu’a ta rigayi fata yaron ya fito ta tsatsonsa ne dan haka yanzu babu yadda zai yi amma a ransa ya fara tunanin bin shawarar Inna ta kaiwa Hassan bakin ruwa dan gaskiya ba zai iya da wannan tashin hankalin ba, gashi mahaifiyarsa ta faɗa masa cewa Hassan mutum ne kawai baiwa ce da Allah ya masa.
Kallon kallo aka shiga yi tsakanin Inna da Imran kowa rai fal tsoro kamar farar kura, ganin jikin yaron ya rikiɗa ya zama miciji kansa ne kaɗai na mutum, hakan ya sa Inna sakin wani fitsari ganinta riƙe da miciji da kan mutum. Sakin uban jikin ta yi ta kama kan kaɗai ta riƙe sai uban jikin ya shige cikin ruwan.
“In..In..Innaaa riƙeshi da kyau kar ki je ki sake shi a ruwan nan ya shaƙi ruwan a hanci da bakinsa ya masa illa ko ma ya mutu” Cewar Imran yana wani zare ido kamar ya ce as ya zura da gudu.
“Ni da zai mutu ma da kowa ya huta” Cewar Inna a zuciyarta a fili kuma sai ta ce.
“Haba Imirana ai na yi jarumta ma da na iya riƙe kan dan na tabbata da kai ne da tuni ka sakashi a ruwan in limewa ma zai yi a ruwan ya lume”
Gabaɗaya kallon ikon Allah suke sai da Hassan ya koma miciji dukansa, har lokacin Inna tana riƙe da kan,hannunyenta riƙe da wuyan micijin, kallonta kawai Imran ke yi so yake ya tashi ya gudu ya barta amma ƙafafunsa sun ƙi bashi haɗin kai, dan duk jikinsa karkarwa yake dan ko jiya ya ga matuƙar ƙoƙarin Inna da ya rufe ta a ɗaki da micijin, dan da ta rufeshi ji ya yi kamar ya mutu saboda fargaba da tsanani tsoro, ga wani mugun tashin hankali da ya tsinci kansa a ciki yanzu kuma ga ta riƙe da kan miciji.Inna da ke ta hawaye tana jan majina a hanci ta ce.
“Wallahi da ace wannan ba ɗan Halima bane da tuni na daɗe da cikawa rigata iska, na haƙura da ZAMAN WANKAN a ce abu ya ƙi ci ya ƙi cinyewa kamar cin tuwon kishiya, kullum jiya i yau, na rantse da Allah da tuni na koma inda na fito gwara gorin Tsalla ya kashe ni dan na san iyakaci ta ce koroni aka yi”
Duk surutun nan da take Imran ba fahimta yake ba so kawai yake ya tsere.
“Imirana, matso ka riƙeshi, sai ka zungureshi irin yadsa Halima ta masa jiya ya dawo mutum” Cewar Inna tana kallonsa.
“Am, uhm, wato Inna ki bari wato ainashin Sadiyar ta fito sai ta zungureshi ai kin san da yake a cikinta ya rayu shi yasa ita in ta taɓashi zai dawo”
“Zancen banza ma kenan, wato haka zan yi ta riƙe da wannan abu… Sai kuma ta yi shiru ta kasa ƙarasawa ganin micijin ya kafeta da ido. Imran ma ya ga hakan sai ya yi saurin aro jarumta ya miƙe tsaye dan kar fa micijin saran Inna zai yi ya san kwa tabbas idan ya gama da Inna kansa zai dawo shi kuma bai shirya mutuwa ba. Inna ganin ya miƙe sai ta gama gane abin da yake shirin yi hakan ya sanya ta tuno da abin da ya mata jiya da dare da kuma alƙawarin cewa sai ta rama da ta yi, hakan ya sanya ta gama shirya abin da za ta masa, musamman da ta tuna cewa Hajiya Amina ta ce wani malami maƙocinta ya ce duk yadda yaron zai zama miciji babu abin da zai yiwa kowa ba zai yi sara ba, sai dai shi miciji ganinsa ma abin tsoro ne gashi da kwarjini musamman wannan Hassan ɗin da girma yake yi sosai idan ya sawaya.
Wata dariyar ƙeta ta yi a ranta, tunawa da irin muguntar za ta masa hakan ya sa ta saki kan micijin da ta riƙe da hannu biyu ta riƙe da hannu ɗaya ɗayan kuma ta miƙa ta damƙo harshen rigar Imran, idanu ya zaro ganin abin da Inna ta yi wani faɗuwa gabansa ya yi da mugun ƙarfi dan ya san matsawar suka haɗa hannu da Inna to tabbas ba za a kwashe da daɗi ba, dama ya lafiyar kura bare ta yi hauka hannu ya sanya zai fincike rigar amma sai ya ji ya kasa domin Inna ta mata riƙon kazar kuku kamar ma ba tsohuwa bace ta riƙe sai ka ce wani ƙaƙƙarfan ƙaton ne ya riƙe masa.
“Ka zaci za ka iya ƙwacewa ko, to ko uwaka Amina na riƙe sai dai ta saduda saboda ƙarfina da naku ba ɗaya bane kuna nan binni kuna cin kayan daɗi wanda basa riƙe ciki ni kuwa ina can ƙauye ina cin tuwo da danbu wanda suke gina jiki”
“Haba Inna bayi fa zan je in shiga ya kika riƙe ni”
“Tusugunno za ka yi ba fitsari ba, ban da rainin wayo ni zaka buɗewa ido to wallahi sai dai ka saki fitsarinka a tsaye kamar saniya, dan ba zan sake ka ba, ni ma nan jigilif nake da fitsarin kayana jargaf kamar na yi iyo a ruwan maliya”
Imran ganin Inna na janyo shi ya sa ya kakkafe tana jansa yana togewa, haka ta janyoshi ta dawo dashi kusa da ita ta ce.
“Sa hannu ka taɓa yaron nan ya dawo mutum”
Idanu ya zaro ya shiga girgiza kai yana roƙonta ta sake shi.
“Ka taɓa shi na ce, ya dawo mutum yo ban sa ma lalacewa ni da nake ɗorin ɗosano ma na taɓashi bare kai”
“Inna ki min rai dan Allah”
“Ranka yana hannun Allah” Cewar Inna tana ƙara damƙe rigar Imran sai da ya gama tsurewa sosai ta ga idanunsa sun fito sai zare su yake kamar wanda ya yiwa sarki ƙarya, aikuwa ta sanya ƙafa ta danne harshen rigar Imran, ta sanya hannayenta biyu ta ɗago Hassan a siffar miciji ta ɗorawa Imran a kan cikinsa da yake data janyoshi kwantawa ya yi reran, haka ta .
ɗora masa micijin kan micijin a wajen sai tin haɓar Imran idanun Imran cikin na micijin.
Imran hatta numfashinsa kasa shaƙa ya yi duk tunaninsa ma yadda aka yi Inna ta shammacesa har ta masa riƙon da ya kasa ƙwacewa.
“Ka sanya hannu ka shafa kansa ya dawo mutum in wankesa kafin uwarsa ta fito”
Ta faɗa tana kallon idanun Imran da ke kafe cikin na micijin dan ya kasa motsa ko da yatsansa ne bare ya iya ɗauke kansa.
“Imran a mace ko a raye? Kai kamar ba namiji ba”
“Wallahi ko maza maza ne ni dole in ɗauke wuta Inna wannan in ban mutu ba ma ai kwanana ne a gaba” Cewar Imran a zuciyarsa hawaye na bin fuskarsa.
Hannu Inna ta miƙa ta ɗan taɓa micijin aikuwa ya ɗan motsa ya kaɗa jela, Imran kuka yake kawai marar sauti.
“Ba ni ka sanyawa abu a fura ba na rinƙa sawu bayi kamar mahaukaciya sabon kamu, daga na dawo wani kashin ya dawo na koma bayin har sai da na dawo na kasa zama da ɗuwaiwukana, ƙarshe sai durƙuson haihuwa na yi, bayan rabona da in yi durƙuson haihuwa tun na naƙudar uban Sadiya amma sai gashi ka sanya tarihi ya maimaita kansa”
Ganin dai ba ya motsi sai Inna ta sake zungurin micijin aikuwa micijin ya fasa kansa kamar zai sari Imran diff kake ji jikin Imran ya saki, ashe suma ya yi, hakan ya yi dai dai da shigowar Sadiya.
Wani salati Sadiya ta saki tana yin kan Imran da sauri, hannu ta sanya ta zunguri micijin aikuwa sai ya dawo mutum tare da sakin kuka ɗaukansa ta yi, ta ɗora a kafaɗa ta sanya hannu ta shiga jijjiga Imran amma shiru kake ji kamar an aiki bawa garinsu.
“Inna garin ya haka ta faru” Sadiya ta faɗa tana sakin kuka cikin tashin hankali. Wata harara Inna ta jefa mata, ta kalleta ta ce to uwar ƴan son miji ba mutuwa ya yi ba suma ya yi, kuma ba komai ya sumar da shi ba illa soyayyar irin ta uba da ɗa ”
Banza ta yiwa Inna ta ajiye Hassan a kan gadonsa da har lokacin bai yi shiru ba ta fita da sauri ta ɗakko ruwa a kofi tana zuwa ta sheƙawa Imran, amma shiru kake ji wai malam ya ci shirwa, sai da ta ƙara masa ruwan sai ya sauke wata ajiyar zuciya ya buɗe idanun yana wani ƙiƙƙiftawa saboda bai gama dawo wa hayyacinsa ba, dariya Inna ta ƙyalƙyale da ita kallonta Sadiya ta yi cikin jin haushi ta ce
“Haba Inna ya haka mutum ya suma kuma kike dariya.
Dariyar dai Inna ta cigaba da yi sai da ta yi ta ishe ta sannan ta ce.
” Barni in dara Sa’adiyya wai baki ga yadda idon Imirana ya yi ƙulu-ƙulu ba, kamar an sanya goruba a cikin kwanon sha, ji fa yadda yake kwance magashinyan ko zaune ya kasa tashi”
“Wai ma garin yaya haka ta faru Inna dan Allah ki bar dariyar nan”
“Baki lura da kyau bane Halima kalli yadda na jiƙe da fitarin tsoro da wahala, to kalli wandom mijinki ma ya saki fitsarin shi ma, amma saboda ragwanta, Imirana har suma ya yi amma ni ina tsohuwa babu abin da na yi, wai fa ɗaukan Hassan ya yi ya ɗora a kafaɗa shi ne kawai Hassan ya koma miciji a kafaɗar tasa wannan ne dalilin da ya sa ya suma kin ga kwa dole na yi dariya ni da bakina Allah ba ya tsaga min ba a hana ni walawa sai ka ce wani kututturen icce”
Cewar Inna dan bata so Sadiya ta fahimci abin da ke faruwa.
Wani takaici ne ya tokarewa Imran jin abin da Inna ta faɗa, hakan ya sanya ya fara yunkurin tashi zaune dan shi bai ma san ya yi fitsarin ba sai da ya ji ta faɗa.
“Kama shi mana Halima, bari in taimaka miki, Imran yana ji yana gani aka kamashi da Inna aka zaunar da shi dan duk jikinsa babu ƙarfi tsoro da fargaba sun yiwa gaɓɓan jikinsa katutu hakan ya sanya gaɓɓan yin sanyi.
Inna sai jera masa sannu take saboda kawai neman magana shi kuma Imran yanzu kawai idanunsa a kan Hassan yake da ke kuka gabaɗaya ji ya yi ya tsorata da yaron, Sadiya ɗaukansa ta yi, ta bashinya sha sannan Inna ta ɗaukeshi ta masa wankansa tas aka yi sa’a bai sawaya ba.
Haka dai aka gyara falon kowa ya gyara jikinsa kafin Ashrof ta zo ta gyagygyara gidan duka, Imran kuwa ya ƙufuli Inna a ransa sosai.
“`DA YAMMA“`
Ƴan barka na ta shigowa ƴan unguwa da kuma dangin Mama da kuma abokan arziƙi, Mama da Hajiya Amina tun da suka yi la’asar suka tafi gida, Imran kuma ya fita ba ya nan, Inna da ta fito za ta je kicin, Imran ta gani ya shigo daga waje waya a kunnansa yana magana bakin nan a washe kamar gonar auduga sai sakin fara’a yake. Kallonsa Inna ta yi, ta wuce abinta, lokacin da ta dawo sai ta same shi yana cewa Sadiya.
“Yanzun nan ya iyo min waya wallahi ya ce suna hanya za su zo shi da matarsa barka ”
“Ikon Allah to yaushe suka zo garin” Cewar Sadiya tana washe baki ita ma.
“Kin san ai yanzu an maido da shi Kano da aiki yana barek ɗin cikin garin nan” Cewar Imran.
“Allah sarki ka ce yau muna da manyan baƙi gaskiya yaushe rabon su da Kanon ma baki ɗaya sun yi zaman su a lagos abin su”
“Wallahi kuwa”
“Bari na duba ko sun zo” Ya faɗa yana juyawa ya fice. Inna ce ta taɓe baki ta kalli Sadiya ta ce.
“Wai Halima in ce dai gwabna ne zai zo gidan nan?”
“Gwabna kuma Inna”
“Yo in ba gwabna ba waye zai zo da kuka ta rarraba haƙwara a tsakaninku sai dariya kuke na ɗauka ai sai gwabna zai zo dan zai raba kuɗi ma ai a yi dariya”
“Kai ke kuwa Inna to abokinsa ne da ya tafi aikin soja, a Lagos yake aiki shekara da shekaru ma yana can tun kan mu haɗu da Abban twins yake aikin soja”
“Soja??? Inna ta tambaya.
Kafin Sadiya ta bata amsa sai jin sallama suka yi, cikin muryar da Hausa bata wadaceta ba an ce
“Assalamu alekum” Mata da mijin suka haɗa baki wurin faɗa. Idanu Inna ta zaro ta kalli Sadiya da ta amsa sallamar ta ce
“Wai Sadiya inyamuraine amma dan daga ji babu hausa a harshensu” Ta faɗa cikin raɗa-raɗa. Kafin Sadiya ta ce wani abu sun shigo tare da Imran, miji ne da matarsa da tsohon ciki sai ƴarsa ƴar kimanin shekaru biyar. Wani ƙato ne baƙi kamar ya shafa shuni.
“Tabɗi danƙari iko sai lillahi, mutum kamar buhun gero, tamkar dusa yake ci”……Cewar Inna da ta zabura ta tashi tsaye ganin girman mutumin.
Masu son a tallata musu hajarsu
09030283375
[24/03, 5:13 AM] Mom Mashkur First class: “`Wannan littafin kuɗi ne 300
Za a tura ta wannan accaunt ɗin Fa’iza Abubakar 0020281885 Unity bank shaidar biya ta wannan no 09030283375 idan katin waya ne mtn Ƴan Niger su tuntuɓi wannan no +22785885134
DAN ALLAH KAR WACCE TA SAYI LITTAFINA DAN TA FITAR MINI,IDAN DAN KI FITAR ZA KI SIYA KI RIƘE KUƊINKI BANA BUƘATA.“`