Nasarar Rayuwata 41
*Talented writers forum*
*41*
Bayan Hajjo ta koma ta kasa fadawa inna zancen Ina zata fara? Kodai ta fadawa maman Nana ta gayawa inna , haka dai ta cigaba da sake sake har tayi Shirin kwanciya ta kasa sanar da ita. Doguwar Rigar bacci ta saka me tsantsi ta fesa turaren body mist nata ta tufke gashin kanta sannan ta dora inner cap tare Sanya safa me kauri da laushi saboda tana Jin sanyi damuna ya fara shigowa. ta duba time 9:24pm tasan Aman Yana gaban system warhaka Yana aiki donhaka Kai tsaye ta fara Neman layinsa , ringing yayi har ya kusa yankewa kafin aka d’aga ” masoyin I’m darm missing…” Kutumar Uba…ke wacece y’ar matsiyata toh tun wuri ki gaggauta fita harkar mijina kafin na konaki da ranki ” murmushi hajjo tayi” aw..mum Fahad ya kike ashe wayar na hannunki toh don Allah dan bashi wayar zamuyi magana ne dashi it’s important ” ke kinsanni kuwa shegiya y’ar iska ke har kin Isa ki bani umarni, toh wallahi kiwa kanki fada ki rabu da Aman, ashe ke kika shiga rayuwata yasa na fara ganin canji tattare dashi toh wallahi kika sake kiransa sai nadau mummunan mataki akanki shegiya me bin mazan mutane ” dariyan keta hajjo tayi ” haka kika ce ,toh shikenan ni Kuma yanzu na fara son mijin naki idan zaki mutu ko zaki rayu duk ya rage naki ,nida shi mutu ka raba Babu Mai rabamu sai Allah ” huci zee take nan ta kashe wayar ta wullar da ita gefe zuciyarta na tarfafasa yau ita zaa ciwa mutunci , bari Aman yazo dole ta taka masa birki chabdi…kalaman hajjo take tunawa tace ” dankari lallai yarinyar nan ta samu guri wato ta samu kan Aman har tana Wani kiransa masoyi ” kasa zama tayi ta fara safa da marwa cikin d’akin Aman ya fito daga wanka daure da towel tana ganinsa ta fashe masa da kuka ” lafiya beb wat happen ”
“Bansani ba munafuki yau asirinka ya tonu Allah ya kama ka Kuma wallahi banyafe ba amanata da kake ci ” didn’t get you sorry ” ya dawo kusa da ita ta dauki wayarsa tana Mika masa ” y’ar iskar da kake soyayya da ita ta kira ni Kuma na d’aga, wallahi ka gaggauta fita harkar y’ar mutane ko na mata illa wallahi kasan halina bani da mutunci ” murmushi yayi kafin yace ” haba beb kinsan dai…
“Keep it to yourself guntun munafuncin naka ” ” haba beb don’t you trust me ” ya karasa ya rike hannayenta suna kallon juna ya jawota ya rungumeta, tana cigaba da kuka yahau rarrashi daga haka labari ya canza ya mantar da ita bacin ran da take ciki.
Washe gari hajjo ta sake Kiran layinsa baa d’aga ba har 2 missed call abinda Bai taba mata ba Kuma Bai kira back ba har yamma tana expecting call nasa amma shiru nan ranta ya baci ta tabbata matarsa ce ta hana wato tsoronta yake ji nan Wani kishi ya turnuketa tasawa kanta cewa zata nuna masa kuskurensa. Gaba d’aya wunin ranar Bata cikin walwala don ko school bataje ba a d’aki ta yini bisa gado sai sallah ne ya tasheta, har wajen after 4 ta fito falo don Neman abinci inda ta tarar da Ayman tare da wata da alama matarsa ce da Kuma y’arsu. tana sanye ne da palazo da fitted top armless sai karamar scarf da ta yafa qamshinta ya fara cika falon kafin ta karasa da sallama, inna tana zaune ta d’aga Ido ta kalleta ” sai yanzu kika ga damar fitowa ” “banjin dadi ne am having a headache” tana magana cikin sanyin murya kafin ta Maida kallonta gun Ayman tace ” Yaya sannu da zuwa Ina yini ”
” Lafiya alhmdllh ya school” fine alhmdllh” ta Kalli Failuzaa a fusge tace ” Ina yini ” “lafiya” ta amsa kamar Bata so , kallon yarinyar tayi kyakkyawa ce me kama da ubanta sak sai hasken maman da ta dauko ” baby girl how are you ” murmushi yarinyar ta mata daga nan ta juya tayi hanyar kitchen hankalinta na kan waya tana dubawa ko akwai missed call na mutumin nata. Satan kallonta Ayman yake don wankan nata ya tafiyar da imaninsa ga Kuma qamshin turaren nata me sanyaya zuciya, lumshe Ido yake cikin zuciyarsa kuwa adua yake Allah ya mallka masa ita. Failuzaa kuwa har cikin zuciyarta taji ta tsani hajjo saboda kyaunta da Kuma salon yadda take magana take taji Wani irin kishi ya diro mata ya Kalli Ayman tace ” ya kamata mu tafi yamma tayi fah ” hararinta yayi ba tare da yayi magana ba inna tace ” haba ke kuwa ko awa guda bakuyi ba da zuwa Kuma zaku tafi ko ruwan gidan Baki Sha ba bare abinci ” hararin kwanukan abincin tayi tana Bata fuska ita burinta kawai suje gida kar ya sake Ido hudu da hajjo. Muryarta ne ya Maida hankulansu gareta tana waya da Ummeey tana rike da plate a rufe da alama abinci zata ci tayi shigewarta d’aki ba tare da ta Kalli bangaren da suke ba , Ayman ya kalleta yace ” ki zubamin abinci kadan ” tabe baki Failuzaa tayi don batayi tunanin cewa zaici abincin ba, ta debo masa white rice da lamb chops and sauce sai Kuma kunun aya nan ta ajiye masa saitin inda yake zaune , duk yadda Failuzaa ta gaji haka ta zauna don sai bayan Isha suka bar gidan inna ta cika ta da kayan qamshi Wanda Ayman yaji dadin Hakan , hajjo kuwa Bata sake fitowa ba har sai bayan da suka tafi.
_________
The next day sun fito lectures din 10am ta hango motar Aman tayi saurin kauda Kai gefe Yana cikin mota ya hangota yai saurin fitowa ya karasa inda suke Bai damu da cewa Ummeey kanwar matarsa bace yaje kusa da hajjo Yana kallon face nata ” am so sorry baby I’ll explain please” murmushi Ummeey tayi lallai ta Kara tabbatar da soyayyar nasu ” Ina kwana Ya Aman” lafiya Ummeey yawwa ki mata magana don Allah kice tayi hakuri please is not my fault ” besty kiyi hakuri ki yafewa Yaya nah” hararinta hajjo tayi tace ” idan bazaki tafi ba zan tafi nabar ki ” tana gama fada ta Kara gaba Aman yayi saurin tare gabanta ” don Allah ki saurareni please beb ” ka daina hadani da Allah ka cuceni malam just go your way na rokeka forget about me please ” ya marairaice” you know I can’t my angel…da zan iya da na dade da barinki but I can’t please find a space in ur heart n forgive me don Allah ki bani chance I’ll explain everything ” no need for that Mr ” Ummeey tayi gaba don Basu guri su tattauna, hajjo ta cigaba da tafiya Aman na.biye da ita duk abunda ke faruwa a idon Ayman Yana Zaune cikin motarsa Wanda yazo shi kadai ko Fauzan baisan yazo ba dama yazo saboda ganin hajjo don jiya dakyar ya samu bacci shiyasa ya biyota school Amma Hakan Bai samu ba. Students sai kallonsu suke yadda Aman ke magiya hajjo kuwa ko kallonsa batayi da ya gaji yace ” kinsan Allah ko ki saurareni ko na rungume ki cikin mutane u know me I mean it” kallonsa tayi ya gyada Kai yace ” yes am serious wallahi kinji na rantse” numfashi ta sauke tasan ba kunya ne dashi ba zai aikata abunda yafi hakan donhaka ta ja ta tsaya ya Sauke numfashi yace ” Kai Yan mata irin wannan ajin idan mukayi aure kina min haka wallahi zaki Gane shayi ruwane ” harara da galla masa tace ” me zakamin mijin tace kawai Allah yasa ta bari ayi auren ma naga tsoronta kake har zata hanaka daukar waya ” “ke kinsani ni ba ragon namiji bane wallahi Babu wacce ta Isa ta juyani, wallahi boye wayar tayi sai yau da taji nace zan fita na sayi wata shine ta fito dashi ” ehh saboda ta rainaka ne ai if not ta ma Isa, Amma wallahi ka ja mata kunne idan ta sake picking call dina I’ll deal with her seriously ”
“Haba madam mijinta fah kika kira ba dole…” Ohh ..so u backing her right, shikenan ya Maka kyau ” kwafa tayi ta juya ta fara tafiya yayi saurin hade hannaye yace ” am sorry mana ki tausaya min wallahi jiya kamar maraya haka na kwanta na rasa meke min dadi a duniya” karyar banza kana can rungume da matarka zaka raina min wayo munafuki kawai ” Wani dariya ne yazo masa ya kyalkyale da dariya yace ” ohh my ..Yau nine wato munafuki iKon Allah beb ashe haka kike da kishi I love that, Amma don Allah ki yarda Dani you know I love n I can’t wait to have you ” a haka suka karasa wajen motarsa suka jingina jiki hajjo sai cika take tana batsewa ya Ciro waya Yana mata hoto tana faman zabga masa harara , Yana ta faman tsokanarta tare da rarrashi ahaka ya samu ya shawo kanta dama ance fadan masoya baya dadewa, take suka shirya tana zuba masa shagwaba sai narke masa take Ummeey tana can tana hangosu suna Bata sha’awa tana fatan samun masoyi irin haka. A bangaren Ayman kuwa hawaye ne ya cika masa idanu yayi saurin shanyesu Yana lumshe Ido Yana Maidasu zuciyarsa na faman suya shi kuwa tasa kaddarar kenan bazai samu abunda yake so ba a rayuwa ya tabbata hajjo ta masa Nisan da har abada bazai taba samunta gara ya nisanci Kansa daga gareta , sauke numfashi Mai sauti yayi nan ya cire waya ya kira Fauzan akan ya samo musu flight tickets gobe zasu koma Jeddah, Yana gama waya ya tada motar yayi reverse Yana kallonsu ta mirror har ya fice daga harabar school din.