Ikraam 50
Ikraam~~ By Khaleesat Haiydar
50…..
“Bani na haifi Ikram ba, don hka ku je ku sami
iyayenta a suleja, kar wani ya kuma kawo min
wnn silly tok din idan baya son bacin raina,
Nonsense kawae” tana kai wa nn ta mike ta fice
masu daga dakin, Khaleel ya juya yana kallon
Aliyu da ya dafe kansa ya dawo kusa da shi ya
dafa kafadarsa yace “dnt wrry bro, nasan ynda
xanyi convincin Mami, kar ka damu” Aliyu ya
dago yana kallonsa snn ya gyada masa kai ya
mike da kyar yace “sae da safe Khaleel its gettn
late” Khaleel ya mike suka fita dakin a tare.
Washegari da Asuba Mami bata amsa gaisuwar
Khaleel ba, ya gama tsayuwarsa a dakin ya fita,
Ikram dake tsaye rike da uniform a hannunta
tace “Mami meyasa baki ce ma yaya Khaleel
komai ba da ya gaisheki, ae na yafe masa” Mami
ta galla mata harara tace “sa uniform din knn,
wae ma me kike yi tun daxu ne Ikram” Ikram ta
shiga saka uniform dinta da sauri, snn ta dauki
safarta da takalmi ta sa. Mami tace “kije ki yi
break downstairs” Ikram ta sauka kasa xuwa
dinnin, xaune ta tarda Khaleel a dinnin din ya
dafe kansa ga tea a gabansa, kujerar dinnin din
da ta ja yasa ya dago kansa da sauri, ta xauna
snn tace “idan kana son Mami ta dinga maka
mgna to ka daina neman tsokanana” harara ya
galla mata yace “fita daga nn wawiya kawae” ita
ma ta hararesa tace “to ba breakfst xanyi in tafi
sch ba” Mikewa tayi da sauri ta dawo gabansa
tana kallon kirjinsa, singlet ne jikinsa sae farar
shirt da bae yi button ba, ta daura hannu a kirjin
tace “lah yaya Khaleel, chest din ka irin na
yayana wllh kalli gashi” sae da yyi baya ya kusan
faduwa ya turata da sauri yace “ke ina wasa da
ke ne” dariya ta kyalkyale da, yyi tsaki ya turata
daga gabansa ya mike ya bar dinnin din. Ta bi sa
da kallo tana murguda masa baki, Karfe hudu da
minti biyar Ikram ta shigo gidan bayan sch bus
ya ajiyeta ta gaida jummae snn ta wuce sama
xuwa dakin Mami, kwance ta tarda Mami a dakin,
duk da idonta biyu bata ma san ta shigo ba,
Ikram ta karasa kusa da gadon da sauri ta
durkusa tana kallon Mami tace “Mami baki je
office bane yau, ko baki da lfya ne” Mami ta
kirkiro murmushi ta mike xaune tana kallon Ikram
tace “har kin dawo dota” Ikram ta gyada mata
kai tace “gud evenin Mami, re yhu sick?” Mami ta
girgixa mata kai tace “am ok dota, yau ban da
aiki ne a office shine nake hutawa, maxa tashi ki
cire uniform dinki kiyi wanka kiyi sllh sae kije ki
karba abincin ki gun Jummai” Ba musu Ikram ta
mike ta cire uniform din ta tana cewa “Mami ni
yau baxan je Islamiyya ba kai na nata min ciwo a
sch, kuma an bani magani na sha” Mami tace
“wani maganin suka baki kika sha” Ikram tace
“wani farin circle magani aka bani na sha da
ruwa” Mami tace “daga yau kar ki kuma shan
magani idan sun baki, xan je in samesu ma, idan
kanki na ciwo ga magani nn a gida” Ikram ta
gyada mata kai snn ta shiga wanka, Mami ta
mike ta fito mata da kayan da xata sa snn ta
koma ta kwanta. Ikram na gama sa kayanta tayi
sllh snn ta sauka kasa xuwa gun Jummai ta
karba abincinta ta dawo cikin falo da sauri ta
kunna TV snn ta xauna tana ci tana kallo. Karfe
biyar Aliyu ya shigo falon da sallama, ta mike da
sauri taje ta rungumesa ta daga kai tana
kallonsa tace “yayana jiya ban san lkcn da ka tafi
ba” Murmushi yyi yace “uhm kin yi bacci ne”
tace “shine baka tasheni in raka ka ba ko, kasan
me yayana, yau an bamu practical da xa muyi a
Home economics kuma nasan yaya Khaleel
baxae koya min ba” ya durkusa gabanta yace
“wani practical aka ba ku” tace “wae Abrasive xa
mu yi” ya mike yace “to xan maki kafin in tafi,
Mami tana sama ko?” ta gyada masa kai tace
“ehh bata je office ba tace min hutawa take yi
yau” ya kirkiro murmushi yana gyada mata kai
snn yace “je kiyi kallonki kafin in sauko” Ba musu
ta koma kan kujera ta xauna ta ci gaba da
kallonta, snn ya haura sama xuwa dakin Momy, a
sanyaye yyi sallama ta amsa snn ya shiga dakin
[2/25, 08:35] Zjy: ~