Ikraam 3
[12/30, 8:39 PM] +234 706 135 1072: ~Ikraam~ By Khaleesat Haiydar 3…… A hanya
ikram ta hadu da su Altine kawarta suna dawowa
daga islamiyya, Altine tace “ina xaki Ikram,”
Ikram tace “kasuwa xanje na ga ko xan ga matar
daxu ta kuma bani Ayaba xo ki raka ni,” Altine
tace “wace mata?” Ikram tace “wata babban
mata ce ta bani ayaba da kudi da apple matar na
da katuwar mota da katon yaro har ya xama
baba shi ma” Altine da ta bude baki uwa sokuwa
tana kallon ikram tace “aa ni gida xan tafi kar
baba tayi man duka,” Ikram ta murguda mata
baki tace “shine kika tsayar da ni,” tayi kwafa
tare da jan tsaki ta ci gaba da tafiyarta, Altine
tace “malam yace me yasa kika daina xuwa
makaranta fa,” Ikram na ci gaba da tafiyarta tace
“Ammi tace baxan kuma xuwa ba,” Altine da
sauran kawayenta suka tabe dan bakinsu suka ci
gaba da tafiyarsu. Ammi na fitowa ta nemi ikram
ta rasa tsakar gidan, ta leka dakinta bata ciki, ta
fito tana haska tsakar gidan ko xa ta ga
takalminta ta ga bbu, ta rike habarta tana girgixa
kai cikin damuwa tace “na shiga uku ni Aisha ina
yarinyar nn tayi kuma” Hijabinta ta figa tayi gun
me treda don nan daya daga wajajen xuwanta,
yace ae ikram bata yo gun sa ba, tayi gidansu
Altine mamar Altine na daki ta fito, tace lah ae
ikram ko bata shigo ba, Ammi tace “to su Altine
fa,” matar ta kwala ma Altine kira ta fito, Ammi
tace “kinga ikram altine,” nn Altine ta labarta ma
Ammi abinda ikram ta gaya mata, Ammi ta fita
daga gidan da sauri tana cewa “nashiga uku na
lalace, kashe ni ikram ke son yi, kasuwa da
daddaren nn?” Mamar altine ta bi ta suka fita ita
ma tana salati, nan suka shiga neman ikram gida
gida a anguwar ko karya tayi ma altine, amma
duk inda suka shiga sae ace bata je ba, hnklin
Ammi duk ya bi ya tashi, mamar altine sae ca
take xa su ganta. Ikraam bata taba xuwa kasuwa
da daddare ba, tana isa ta tarar duk an kulle
kofofin shiga cikin kasuwar nan ita wae gun mae
fruit din xata je ta tambayesa ko matar ta sake
dawowa, wani mutumi dake xaune yana xukar
wiwi da yan uwansu su kusan hudu kan benci
taje ta sama tana kallonsa tace “kai meyasa aka
rufe kofofin nn, waye kuma ya rufe gashi ina son
shiga,” mutumin ya daga jajayen idonsa yana
kallonta da mamaki yace “shiga xa ki yi?” tace
“eh mana gun mai Ayaba nake son xuwa,” duk
suka bushe da dariya ta dinga binsu da kallo baki
a sake, wani daga cikinsu ya fixgota yace “xo mu
je in nuna maki idan xaki bi ki je gun me ayaba
yarinya,” sauran duk suka kuma kwashewa da
dariya ta fixge hannunta tana murguda masa dan
karamin bakinta tace “dan iska kawae,” ya buda
ido ssae yana kallonta yace “ni kika ce ma dan
iska?” tace “eh mana ae ku duk yan iska ne
nasani, dama Ammina tace min duk masu shan
sigari yan iska ne kuma basu da mama da baba,”
ta kuma murguda masu baki tana jujjuya mnyan
idanunta ta ja wani dogon tsoki ta koma jikin
karfen kasuwar ta shiga hawa wae xata dura ciki,
har ta kai tsakiya gnin ynda suke ta dariya yasa
ta sauka ta juya xata bar wajen, mutum biyu
suka fixgota a tare, wani kuma ya shake wuyarta,
ihu ta fasa, wani ya mike ya daga ta sama da
katon muryarsa yace “ku xo mu je,” duk suka
mike, ta dinga ihu tana shure shure, wani bawan
Allah ya xo wucewa ya bisu da gudu yace “ina
xaku kai yarinyar,” ikraam tace “wllh yanka ni
xasu je suyi yan iska ne su, sigari suke sha,”
gabansu ya shige yace “maxa ku ajiyeta,” duk
suka bushe da dariya wani yace “kama gabanka
malam,” wani wawan naushi ya kai ma wnda ke
rike da ita ba shiri ya saketa ta fadi kasa, ta
mike a guje ta bar wajen, mutane biyu suka bita
da gudu, sauran suka rufe mutumin da duka, kan
kace me har ta bace masu don lungu lungu ta
dinga bi gashi ta iya gudu, tana mayar da
numfashi ta iso anguwarsu duk ta jefar da
takalman kafarta da hula, anguwar tsit gun mai
treda ta nufa tana kallon kofar gidansu kmr
munafuka, bata tarar da shi ba amma shagon a
bude yake, ta xauna kan benci ta kara fitilar da
ya rage snn ta dauki sweet daya ta jefa bakinta,
ta kai minti kusan talatin xaune a gun, jifa jifa
tana ganin mutane da fitila suna wucewa sae ta
buya, ashe nn duk nemanta ake, muryar mai
treda taji da wasu maxa guda hudu suna cewa
“idan Allah ya yrda ma xa’a ganta, bbu abinda ya
sameta,” mai tredan yace “to Allah yasa hka, ban
jin ma xan iya xama shago ynxu bari na rufe
kawae na tafi gidan wllh rashin ganin yarinyar nn
ya tsaya min a rai,” ya karaso cikin shagon xae
kashe fitila ya rufe ya ga ikraam xaune tana
kallonsu, sae da ya koma baya da sauri da
mugun mamaki yace “ikraam” ta washe hakora
tana kkrin boye sweet din hannunta, yyi waje da
sauri cikin daga murya yake cewa “jama’ah ku xo
ga ikram a shagona,” baban altine ne ya fara iso
wa da sauri snn sauran makwabtansu, me treda
dae na tsaye baki bude yana kallon ikram, baban
altine ne ya hade rae yace “daga ina kike Rabi,”
ta dan marairaice tace “kaga baban altine a nn
kofar gida ne wasu masu shan sigari suka daga
ni sama shine na shigo shagon baba Habu da
gudu, amma sun tafi,” Ammi ce da su maman
altine suka karaso wajen da sauri, Ammi ta ci
kuka har ta gode Allah.