Hausa NovelsIkraam Hausa Novel

Ikraam 11

Sponsored Links

Ikraam~ By Khaleesat Haiydar 11…… Tana gama fadin hka ta fara tafiya, ya riko hannunta da sauri yace “aiken ki mama tayi” ta girgixa masa kai tace “A’a ni dae xan je ne ya bani Ayaba” ta fixge hannunta xata tafi yyi saurin rikota kuma yana kallon dan hawayen dake idonta yace “wa ya doke ki Ikram” Ikram tace “ba Ammi bace tace Hinde ta tafi dani gidansu gun kawu na lado kuma mugu ne shi, shine na gudo abuna” yasa dan yatsa ya share mata hawayen yana kallonta yace “to meyasa tace a kai ki” ta dan tabe baki tace “sbda wae na tafi yawo jiya, kuma ai ba yawo na tafi ba Anty ce ta kai ni gidansu” ta fixge hannunta xata yi gaba ya fixgota yace “ke wae ina xaki ne” tace “A’ah nace maka gun me Ayaba xani ya bani mana” ya ciro da chocolate daga aljihunsa ya mika mata yace “kina son wnn?” ta karbe da sauri tace “ehh ehh ina so” yyi murmushi ya xaunar da ita gefensa yace “to xauna ki sha, da ddi ssae” ta shiga bude chocolate din da sauri ta fara ci, tace “umm ddi” ya gyada mata kai snn yace “to dan tsammin mana” ta sa a baki ta gutsura kadan da hakorinta snn ta fito dashi jagab da miyau ta mika masa, ya galla mata harara yace “bana so, wnn na hannunki nake so” ta murguda masa baki tace “to kar kaso, ni kuma baxan bada ba” xata mayar da wanda ta gutsura masa baki, ya fixge da sauri ya sa a nasa bakin, tace “Allah ya taimake ka yaro” dariya ssae yyi, yana ta kallonta tana cin chocolate tana wani lullumshe ido, har ya kare snn ta bude idon tana kallonsa tace “dadi wllh, ka bani wani mana” xae yi magana ya ga tayi bayansa da gudu ta durkusa ta daura fuskarta kan bayansa ta boye, yace “me ya faru” a hankali tace “mai treda ne na gani, kuma xae iya gaya ma Ammina ya gan ni a nn kasan ya iya gulma” murmushi kawae yyi har mutumin ya wuce su snn ta dawo gefensa ta xauna tace “ka bani wani mana don Allah” yace “baki tambayeni Mami ba” da sauri tace “ina take” yace “gobe xata xo gidanku” Ikram ta yo waje da ido tace “me xata xo tayi” wayarsa yyi ring ya ciro tace “lah kai ma kana da waya,” ya daura hannunsa kan lebbenta yace “shiii” shiru tayi ya daga kiran tana ta kallonsa har ya gama, snn ya mayar cikin aljihunsa, ta kamo hannunsa ta dan marairaice tace “don Allah xo ka ban wayar mana” ya xaro ido yace “kai me xaki yi da shi?” tace “nima waya xan dinga yi mana” ya tsura mata ido yana kallonta ta hura masa iska, ya dauke kansa da sauri tace “meye kke kallona hka” ya harareta yace “meye xaki hura min iskan bakin ki a fuskata” ta mike tace “ni dae na tafi gun mai ayaba kafin dare yyi” ya mike shima ya kama hannunta yace “to muje in raka ki” suna tafe tana basa lbrin ynda ta gudo daga gidan kawu na lado sae dariya yake har suka iso kasuwar yana rike da hannunta suka isa gun mai fruit xama tayi niyyar yi abunta tayi masa surutunta kmr ynda ta saba ya bata Ayaban, Aliyu ya basa kudi ya karbi bunch daya ta shiga tsallen jin dadi, ya rankwashi kanta yace “to ca aka yi maki naki ne” ta fixge hannunta kmr xata yi kuka tayi gun mai ayaban dake ta dariya tace “in baka lbri xaka ban Ayaba” fixgota Aliyu yyi yace “kin fiye surutu ikram, wasa nake maki naki ne” sae da ya bata ledan ayaban ta rike snn ta yrda nata ne suka kama hanyar gida tana jin ddi, dai dai gun dakalin nn suka tsaya ya durkusa gabanta ya dafa ta yace “xan tafi Ikram, idan Mami ta xo gobe kar ki ce baxa ki bi ta ba kinji kanwata,” ikram tace “to,” ya ciro chocolate biyu ya mika mata ta karbe tana washe hakora ta juya a guje tayi gida, yana kallonta ta shiga gidan snn ya juya ya bar anguwar. Ikram na shiga gidan cikin xaure ta xauna bayan ta sa sakata a hankali ta shiga cin ayabarta, ta ci yafi biyar amma bata ji ya isheta ba, sallamar shatu taji tana jijjiga kofar xauren da karfi ta labe jikin bango Ammi ta shigo xauren tana cewa “waye hka” a fusace cikin daga murya shatu tace “ki fito ki bani Naira ashirin dina kar nayi maki rashin mutunci a kofar gida yau” Ammi ta bude kofar da mamaki tace “A’a maman Hinde me ya faru hka” Shatu tace “maxa fito min da ashirin dina ki bani” Ammi ta kasa fahimtar me shatu ke nufi, shatu tace “yo wnn barauniyar yar taki ce na ba ashirin ta siyo min magi ta gudu min da kudi, kuma wllh sae na karya mata wuya na kamata” Ammi ta kunce bakin xanin ta ta ciro ashirin din ta mika mata, ta fixge tayi gaba tana huci, Ammi ta kasa barin wajen tace “na shiga uku ni Aisha wnn wacce irin yarinya ce Allah ya bani” a hankali ikram dake labe har lkcn jikin bango ta mike cikin sanda tayi cikin gida da gudu, Ammi ta juya da sauri jin motsi taga bawon Ayaba baje cikin xauren, cikin gida tayi da sauri amma har ta shige daki, Ammi ta tura kofar dakin ta ganta tsaye sae rawa jikinta yake, tana ganin Ammi ta fasa ihu tana cewa “don Allah kiyi hkuri Ammi wllh kudin faduwa yyi shine na gudo gida naga Ayaba a xaure, wayyo Ammi kar ki dokeni don Allah” Ammi ta juya cike da takaici ta bar dakin, sulalewa kasa tayi gabanta na ci gaba da faduwa, tana nn a hka har aka kira Maghrib ta fito da dan butarta tayi alwala ta tarar Ammi ma na alwala a tsakar gidan.
~Ikraam~

Back to top button