Adandi Hausa NovelHausa Novels

Adandi 45

Sponsored Links

*45*
Itama Mama Mairoh miqewa tayi ta fito dagudu ta nufoshi ya tsaya yana kallonta kawai sai suka kama hawaye daqyar Mai martaba ya rarrashi Dad itakuma Mama Mairoh fulani Amina ta kamata suka koma dakinta Samha kuka kawai takeyi ashe dama Mama Mairoh itace mahaifiyar ta shiyasa abubuwa da yawa nata yake yanayi da nata? Ashe dama shiyasa kullum Abdu yake fada fada mata cewa Mama Mairoh tanada muhimmanci a gurinta ashe shiyasa takejin qaunarta a zuciyarta?.

 

 

Daqyar Maina Abdu ya lallabata da kalamansa da salonsa yajata suka koma daki ya fara luguiguiceta har yasamu ta saki jikinta suka farantawa juna.
Mamy kam baa dawo da gawarta gdan sarautar ba a asibitin aka shiryata aka kaita makwancinta da lallashi da komai Dad qin zuwa yayi jana’izarta, kwanaki uku tsakani Dr Hasina ta shige gaba aka mayar da auren Dad da mahaifiyar Samha da ita da Samha suka rinqa kimtsa amarya Mama Mairoh a ranar ne kuma fulani Hadiza tayi nadama ta rinqa binsu tana kuka tana neman gafararsu saboda gabadaya rayuwa tayi mata zafi babu inda take samun sauqi daga gurin jama’ar gdan har Mai martaba bayan ta nemi yafiyar kowa an yafe mata Mai martaba ya rattaba mata saki daya aikuwa tarinqa kuka tana neman ya taimaketa ya yafe mata wlh ta tuba tabi Allah saida Samha da Dad suka shiga sannan ya hqr yabarta a dakinta ya mayar da ita.

 

 

Haka rayuwa taci gaba da tafiya watan yan uku shidda a duniya saiga bullar ciki a cikin Samha aikuwa akayita murna aka rinqa tattali da rainon cikin nan cikinta nada wata hudu akayi bikin Rahmah da Ja’afar wata daya tsakani akayi na qanwar mijinta Yesmin da Mansoor sosai Nasir ya nemi yafiyar Samha shida Ja’afar tace babu komai ai ya wucce qaddararsu ce hakan Mainah Abdu ne yace shi be yafe ba sai sunyi yari na wata shidda shidda sukayi dariya sukace “ai saboda Gimbiya zaa yafe mana” yayi murmushi yace “ya wucce” haka rayuwa taci gaba da tafiya ta kowanne bangare sai son barka, abin mamaki watanni goma da mayar da auren Dad da Mama Mairoh takama rashin lfy ranar itama Samha yini tayi tana fama da labour hankali duk yanakan Samha aka dauketa aka tafi Asibiti ta haifi yaranta biyu dukka mata murna a gdan sarautar baa cewa komai suna dawowa aka sanar dasu wai Mama Mairoh ta haifi da namiji me kama da Samha wayyoh zo kuga murnar gurin Samha itama tayi qani tama manta da haihuwa tayi ta tafi bangaren babar tata taga yanda Dr Hasina taketa kula da jaririn da uwarsa abin gwanin gwasama.

 

Dr Hasina itace take kula da Samha mace me halin yan aljannah babu mugunta babu ojoro gyarata takeyi kamar yar cikinta haka akasha sunan Nusrah da Nuzrah Wato Hasina da Amina tare da qaraminsu babbansu wato Maheet asalin sunan kakansu Mainah Abdu da Samha yaci na wajan iyayensu mata Jabiru.

 

 

Watanni sukayita turawa rayuwa tayi yanda akeso har shekaru haihuwa ta tsayawa Samha cak Nusrah da Nuzrah har sun tafi primary a kuma wannan lkcn ne Dr Hasina ma ta haifo musu qanwa mace wadda akasha shagali murna babu Wanda ta bari har Fulani Hadiza data saki jiki ta koma mumina ta gaske kullum tana tare da yaran da farko basu saki jiki da itaba sai daga baya da suka fahimci tuba tayi me tsarki, ranar suna yarinya taci sunan Maryam suna kiranta da Gimbi.
Rayuwar Mainah Abdu da iyalansa abar sha’awa ga kowa shekaru sunata tafiya cike da alkhairai aikinsa gaba daya ya koma England saboda haka ya debe yaransa da matarsa suka koma can ya sama musu makaranta sukaci gaba da rayuwarsu acan cikin farin ciki tattali da qaunar juna.
Shekararsu uku a qasar Samha ta sake haihuwar auta ta kuwa dage saida akayiwa fulani Hadiza takwara wayyohh dadi a gurin fulani Hadiza wannan ya taga gata takanas ta taso tazo taga takwararta tayita kuka tana qara roqon yafiyar Mainah Abdu don shi tafi cutawa yace ai tama dauka wani abu bai taba faruwa ba rayuwa kenan dama haka duniya take kowa da zamaninsa.

 

 

*_Tammat bi hamdullah_*

 

*Nan na kawo qarshen wannan labari me taken ADANDI kurakuren dake ciki Allah ya yafe darrusan dake ciki ubangiji yasa su isa inda akeso su isa na gde da kasancewa tare dani.*

 

_Don shawara ko neman qarin bayani zaku iya tuntunata ta wannan number_: _09013718241_

 

 

*UMMUH HAIRAN CE…✍*

Back to top button