Hausa NovelsIkraam Hausa Novel

Ikraam 94

Sponsored Links

Ikhram~ By Khaleesat Haiydar 94…. Khaleel ya sakko kasa yana ma Maryam mugun kallo, ta dauke kai tana rike da kugunta, ya juya yana kallon Ikram da taki karasowa kusa da Maryam din sae fitsara take xaxxaga mata daga inda take tsaye tana tafe hannu, ya karasa kusaa da ita ya dauketa cak ya wuce sama da ita tana cewa “ni wllh ka kyaleni in gwada mata hankali” dakinsa ya bude ya kwantar da ita kan gado sae huci take kmr wata xaki, ya koma ya rufe kofar dakin ya dawo ya xauna kusa da ita yana kallonta yace “tunda ba kya tausayina ikram nima na daina tausayin ki daga ynxu, yau da daddare dolen ki ki bani hakkina, ba suma ba ko mutuwa ma kiyi baxan tausaya maki ba tunda nima ba tausayin nawa kike ba” nn da nn ta nutsuwa gabanta ya shiga faduwa ta mike xaune kmr xata yi kuka tace “ba hka bne ya Khaleel ni bana son kishiya ne kuma….” sae ta fashe da kuka, ya rungumeta yace “Maryam ba kishiyar ki bace Ikram yayarki ce, sae da tayi min alkawarin baxata yi kishi dake ba snn na aureta, don Allah ikram ki bata hadin kai ku xauna lfya xata koya maki abubuwa da yawa plss My Ikram” Ikram ta turo baki tace “to me ta iya da ni ban iya ba da xata koya min” ya bata rae yace “ohh baxa ki ce min to ba?” da sauri ta karyar da kai tace “to” yace “yauwa kanwata, kinga idan kina jin maganata baxan sake cewa xan maki komai da daddare ba tunda bakya so, taso muje muyi break fst” ba musu ta mike ta bi bayansa suka sauko kasa, Maryam na kitchen ya shiga kitchen din yace “dinnin xaki ajiye break din Maryam” ya fito ya kama hannun Ikram dake tsaye suka nufi dinnin ya ja mata kujerar kusa da inda xae xauna, ta xauna shima ya xauna, Maryam na gama jera abincin a dinnin ta ja kujera ita ma ta xauna, da kansa ya deban ma Ikram dankali da kwae ya hada mata tea snn ya debi nasa, Maryam ma ta debi nata. Har suka gama break din Ikram bata bar hararan Maryam da take ba, Maryam dae bata ko kalleta ba ta kwashe kwanukan da suka yi amfani da shi ta nufi kitchen, Khaleel yace “ba kince xaki dinga jin mgna ta ba Ikram” da sauri Ikram tace “ina ji mana, me nayi kuma” yace “to meyasa kike hararanta” ta dan bata fuska tace “to na daina” yace “yauwa to tashi kije ki taya ta ku wanke kwanukan ki ga ynda xata gyara kitchen din” ba musu ta mike ta nufi kitchen din ya bi ta da kallo har ta shiga snn ya sauke ajiyar xuciya ya jinginar da kansa jikin kujeran da yake xaune.
[2/25, 08:43] Zjy: ~Ikraam~ By Khaleesat Haiydar

Back to top button