Ikraam 34
~Ikraam~ By Khaleesat Haiydar 34….. Khaleel ya kai mata rankwashi yace “an dokeki din doluwa kawae” Mujaheed ya fixgosa yace “hw dare yhu, me tayi maka ka doketa beside ina abun duka a jikinta idan ba muguntarka bace ta motsa” Khaleel yace “wonderful yaushe ka xo Jaheed, hope ka taho min da files din jiya, yauwa taho muje ka ga abinda nake gwada maka jiya ka kasa gnewa” Mujaheed ya turasa gefe yace “nt until yhu tel her srry” fixgosa Khaleel yyi suka fice daga kitchen din, ta bi su da kallo tana murguda baki ta share hawayenta tace “duk bana son ku, ni nafi son yayana kuma sae na gaya ku dashi” tayi tsoki tana rike da dan kugunta, Jummai ce ta shigo kitchen din tace “Ikram maxa taho kiyi wanka ki ci abinci” ba musu ta bita tana rike da hannunta suka haura sama, dakin Mami ta shiga da ita don nan take wanka, Mami na xaune gaban computer sanye da medical glass dinta, Jummai tace maxa shiga kiyi wankan na hada maki ruwa, a dakin Ikram ta fara kkrin cire kayanta, ita dae jummai bata ce komai ba, Mami tace “No dota ban hanaki cire kaya kafin ki shiga wanka ba, maxa ki shiga ciki ki cire” Ikram ta dan turo baki ta shiga bayin. Karfe takwas da rabi na dare Mujaheed ya shigo dakin Mami, ko kadan Mami bata bar Ikram ta fita xuwa falo ba tun bayan shigowarta tare da jummai, har lkcn Mami na gaban computer, yace “aiki kike yi ne Mami” tace “wllh kuwa” yace “ae da ki ba Aliyu yyi maki” Mami tace “A’a wanda ke gabansa ma ya ishesa” xaunawa yyi yana kallon Ikram dake xaune can gaban Tv tana kallon cartoon sau uku Mami na cewa ta koma kan kujera ko kan gado amma da ta sake juyowa sae taga ta koma gaban Tvn ta xauna, hkn yasa ta kyaleta kawae, Mujaheed yace “duk kallon ne hka pretty” Ikram da bata ma san da shigowarsa ba ta juya tana kallonsa tace “ehh” yyi murmushi ya juya ya dan saci kallon Mami ya ga ta sauke glass ne tana kallonsa, dariya abun ya so basa yace “Mami xan koma gida wllh duk Khaleel ne ya bata min lkci hka” Mami tace “to Allah ya kiyaye ka gaida mum dinka” yace “tohm xata ji, Ikram ta so muyi sallama mana” Ikram ta juya tana kallon Mami ta ga kallonta take ta girgixa masa kai da sauri, ya juya yana kallon Mami, Mami ta dauke kanta ta ci gaba da abinda take, murmushi yyi, yyi ma Mami sae da safe ya fita daga dakin yana kallon Ikram dake daga masa hannu a boye. Sae a snn Mami ta bar Ikram ta sauka xuwa falo taje ta kalli cartoon din a can don news take son kallo ita, xaune ta tarda Khaleel a falon yana kallon American film ta karaso kusa da shi tace “yaya Khaleel, wae Mami tace ka sa min cartoon” yana gyada kai yace “to xauna, ana gama wnn xaki ga an fara cartoon,” tace “to ae a Mbc3 ne ake cartoon ba wnn ba, hka Mami tace min” ya galla mata wani mugun harara yace “bace a nn, robot xan sa maki ba cartoon ba” da gudu tayi sama tana kuka ta shiga dakin Mami, Mami ta canxa mata xuwa cartoon tace kyaleni da shi je ki xauna kiyi kallonki, taje ta xauna da sauri. Karfe goma Mami ta kashe Tv bayan ita ma ta gama abinda take tace hau gado ki kwanta Ikram gobe da sch, kmr xata yi kuka ta hau gado ta kwanta a hankali tace “Mami yayana ban ganshi ba yau” Mami tace “bacci nace kiyi ba surutu ba” khaleel ne ya shigo dakin ya tsaya daga bakin kofa yana kallon Mami a sanyaye yace “gudnyt Mum” tayi murmushi ta mike xaune sanin bbu daren da bata xuwa dakinsa ta tabbatar ya ci abinci ko bbu abinda ke damunsa snn tayi masa gudnyt ta fito, amma tunda ta samu Ikram ta watsar da hkn, juyawa yyi xae fita tace “am srry son na manta ne hope kaci abinci” ya juya yana kallonta kmr xae mata kuka yace “duk kin watsar dani a gidan nn Mami, ban san ko gajiya kika yi dani ba” Ikram ta mike xaune tace “to kai karamin yaro ne?” dariya ssae Mami tayi shi kam tsayawa yyi kallon Ikram fuskarsa a daure kmr xai shaqeta, Mami ta kashe wutan dakin tace “to kai kaji, in ka fita ka rufe mana kofar dae” washegari da yamma Ikram na xaune tana kallon cartoon bayan ta dawo daga sch, assignment din da Mami tace taje tayi da kanta ta ajiyesa bayan kujera gaba daya hankalinta na gun kallo ko kifta ido bata son yi sbda kallo, budewar kofar da taji don bata ji shigowar mota ba yasa ta mike tsaye da sauri kuma a tsorace a tunaninta Khaleel ne, don daxu da safe ca yyi sae ya mata dukan tsiya abinda tayi masa jiya da daddare, da gudu taje ta rungumesa cike da murnar ganinsa kmr xata yi kuka tace “yayana ina ka tafi na daina ganinka” ya durkusa gabanta ya daura mata lips dinsa kan goshinta ya sakar mata murmushi, ita ma hkn tayi masa ya rungumeta yace “Mami fa” tace “Mami tana sama tana danna computer,” yace “wa ya gaya maki sunansa computer?” tace “Mami ce ta fada min da safe tace har da mouse, da emm” ta juya da sauri tace “bari in tuna” can ta kuma juyowa da sauri tace “keyboard, da c.p.u” ya rungumeta yace “waw kanwata yhu re vry sharp” hannunta ya kama suka nufi dakin Mami, bayan sun gaisa da Mami tace “jiya munje gidanku da Ikram kuwa” mikewa yyi da sauri ya xaro ido yace “gidanmu Mami? Da gske kike Mami? Ohhw God Meyasa kika kai ta Mami.”
[2/25, 08:35] Zjy: ~Ikraam~