Ikraam 33
By Khaleesat Haiydar 33…..
Mujaheed ya wara idonsa ya karaso gaban
Ikram ya durkusa ya kamo hannunta yace “da
gske pretty” tana washe hakora tace “ehh
mana, Allah kayi kama da shi” ta shafa sajensa
tace “shima yana da irin nn hka ma Yaya
Khaleel amma ni bana son yaya Khaleel din nn
sbda kullum….” kwace hannunta Mami tayi
daga na Mujaheed da ke kallonta wit much
interest, ta hade rae tace “bana son hka, maxa
nemi square root dinka” Murmushi yyi ya mike
har lkcn yana kallon Ikram yace “to Allah ya
baki hkuri Mami amma ina kika samo yarinyar
nn wllh she’s so cute” ba tare da Mami ta
kallesa ba tace ‘ya ta ce” dariya yyi yana kallon
Ikram yace “pretty ya sunanki?” Ikram tace “ni
sunana Rabi’a amma Ammi da Abba da ‘yan
anguwarmu suna ce min Ikram, Ammi tace….”
hararanta Mami tayi tace “rufe min bakin nn,
ban hanaki surutu da wnda baki sani ba” Ikram
tace “to ae naga yana kama da yayana ne, in
gaya masa?” Mami ta rungumota bata ce mata
komai ba tana duban agogo, Mujaheed yyi
murmushi xae yi mgna sae ga Hajiya ta fito
daga Kitchen tana kallonsa tace “Mujaheed ina
sakon da na aike ka jiya” ya juya mata baya
yace “mum na ba Aliyu” tace “Aliyu na aika ko
kai” Mujaheed yace “ban samu xuwa bne shi ne
na basa ya siyo maki” tace “to yyi maka kyau,
ae da uwarka ce ta aike ka baxa ka ce mata
baka sami xuwa ba, dan rainin hankli” tana
kaiwa nn ta haura sama, murmushi yyi ya
xauna yana kallon Mami yace “wae Momy kike
jira Mami” dae dae nn Momyn ta shigo gidan,
ba karamin farin ciki tayi ba ganin Mami, ta
wuce sama da su xuwa bedroom dinta, sae
kallon Ikram Matar take, bayan ta kawo masu
ruwa da lemo da kayan ciye ciye take tambayar
Mami inda ta samo Ikram, Mami tayi murmushi
tace “sae dae munyi waya Hajiya,” matar tace
“to shknn, oga Khaleel fa yana nn ko ya koma?”
Mami tace “aa yana nn, ni ban san irinsa ba
sau biyu nake cewa yaxo nn sae yace min ya
xo ashe baya xuwa daxu su Seeyama ke fada
min” Saiham ce ta shigo dakin tace “lah Mami
yaushe kika xo shine baki nemeni ba ko” Mami
tayi dariya tace “ae na tambayeki aka ce kinje
saloon” cikin girmamawa ta gaida Mami tana
kallon Ikram da ta rungume hannunta ta tsuke
baki ita nn fushi take bata gama gaya ma
Mujaheed sunanta ba. Karfe shidda saura Mami
tayi sallama da Momy tace xasu tafi, ta rakosu
har compound suna hira, Mujaheed da ke tsaye
balcony yace “Mami kawo in maki drivin din”
ba musu ta mika masa makullin ya nufi motar
yana yafito Ikram, da sauri ta bisa ya bude
mata gaban motar ta shige shima ya shiga
driver sit, snn ya juya yana kallonta yyi
murmushi xae yi mgna ta riga sa, tace “dama
Ammi tace min kawu na lado ne yace a samin
Rabi’a sbda sunan…..” Mami ce ta bude motar
Ikram tayi shiru da sauri, Mami ta hade rae
tace “me kike yi nn Ikram” Mujaheed da sae
kallon Ikram yake yace “sunanta fa take gaya
min Mami” cikin fada Mami ta fara mgna “ni fa
bana son hka Mujaheed, bani makullin motata
ka fita wnn ae wlknci ne kke min” da sauri
yace “don Allah kiyi hkuri Mami ba fa ni na
tambayeta ba wllh” cikin tsawa Mami tace
mata “dawo nn” kmr xata yi kuka Mujaheed ya
bude mata motar ta fita snn ta dawo baya ta
shiga, Mami ma ta shiga, Mujaheed ya tada
motar yana murmushi suka bar gidan. Har
suka isa gida Ikram bata ce komai cikin motar
ba tana rungume da hannayenta, yana gama
parkin Mami ta kamo hannunta tana murmushi
tace “yhu re sulkn ko dota” Ikram ta sunkuyar
da kanta kmr xata yi kuka, Mujaheed dae sae
kallonsu yake, Mami ta rungumeta tace “to yi
hkuri dotana” fito da ita tayi daga cikin motar
suka yi cikin gida, Mujaheed ya kulle motar ya
bi bayansu. Kitchen Ikram ta nufa Mami tace
“ina xaki” ba tare da ta juyo ba tace “ni ruwa
xan sha” tana shiga kitchen din ta juya tayi
facin din bango ta shiga rera kuka a hankali
amma fa ba hawaye, sae faman murxa idon
take, muryar Khaleel taji a kitchen din yce “ke”
ta juya da sauri ta karasa kusa dashi kmr xata
yi kuka tace “yaya Khaleel shi ne Mami tayi min
masifa” sae kuma ta fashe da kukan tana
kallnsa, juyawa yyi kmr baxae ce mata kmai ba
sae kuma ya juyo yana kallnta yace “me kika
yi?” hawaye na bin cheeks dinta tace “wae don
wani mutumi ya tambayeni sunana na gaya
masa duka” Ya xaro mata ido yace “kika ce
masa sunanki Rabi’a Mama da baba da yan
garinku na ce maki Ikram, kawu na lado ne
yace a sa maki Rabi’a, ke bakya son kawu na
lado…..” cikin tsawa yace “ko ba hka ba?” ta
marairaice tace “ehh amma bata bari na gama
gaya masa ba ae tayi min masifa” ya dan duka
yanda xae iya kallon fuskarta da kyau ya ce “to
daga yau aka sake tambayarki sunanki kika
tsaya bada lbrin kawu na lado sae na….” ba
karamin tsorata tayi ba don daga hannu yyi
kmr xae kwade ta tayi baya da sauri ta juya
xata fice daga kitchen din da gudu, ya rikota,
kuka ta fashe masa da ya daura yatsunsa biyu
kan lebbenta yace “shhii” ba shiri tayi shiru,
yace “kin ji me nace maki” Mujaheed ne ya
shigo kitchen din yana kallon ikram ya karaso
inda suke da sauri yace “pretty wa ya doke ki”
ta fashe da kuka ta nuna masa Khaleel tace
“gashi nn”