Hausa NovelsIkraam Hausa Novel

Ikraam 31

Sponsored Links

Ikraam~ By Khaleesat Haiydar 31…… Mami da kanta ta shimfida tabarma ta xauna tsakar gidan bayan sun shigo snn Ikram ta xauna gefenta don Ammi tsaye tayi inda take kmr an dasa ta tana binsu da kallo jikinta a sanyaye, sae da Mami ta gaisheta snn ta kirkiro murmushi ta jawo karamar kujera ta xauna tayi mata sannu da xuwa, Ikram tace “Mami da yaya Khaleel kika xo,” Mami ta girgixa mata kai tana murmushi, ganin Ammi tayi shiru yasa Mami tace “to Mmn Ikram gani dae na dawo” Ammi tayi murmushi tana gyada mata kai tace “nayi masa mgna ya kuma amince Hajiya” Murmushin jin ddi Mami tayi snn ta shiga mata gdya, Ammi dae sae kirkiro murmushi take, Karfe biyar saura suka tashi tafiya, Mami ta ciro kudi mai yawa ta mika ma Ammi, Ammi tace ita ba don a basu kudi ta bata Ikram ba, dole yasa Mami ta mayar da kudinta, har sun kai kofa Ammi tace “to ajiyarki na jiya fa Hajiya” Mami tace “ni sbda Allah na baku mmn Ikram, ba don kun ban yar ku in rike ba” tana fadin hka ta kama hannun Ikram dake daga ma Amminta hannu kmr xata yi kuka suka fita, Ammi ta bi su da kallo hawaye na bin kuncinta, anya kuwa hkn da tayi dai dai ne, komawa tayi kan tabarma ta xauna jin kafarta sun kasa daukarta ta rafka uban tagumi tana hawaye, ta bada Ikram ba tare da yrdan Mahaifinta ba, to ko ya xa su kwashe ynxu idan ya dawo, wata xuciyar tace kawae tace nemarta tayi ta rasa, mikewa tayi da sauri ta fita ta kira Almajira ta basu kayayyakin abincin da Mami ta kawo suka nufi gidan yakumbo da shi tana biye da su a baya, tasan Babn Ikram na ganinsu xae san bada Ikram tayi ba nemanta tayi ta rasa ba kmr ynda ta yanke hukuncin xata gaya masa, tasan kuma Yakumbo xata fahimce meyasa tayi hka. Dae dae wani makeken gida kmr na Mami driver yyi horn kmr ynda Mami ta umarcesa da yyi, aka bude masa gate ya shiga yyi parkn a parkn space, Ikram tace “Mami ae nan ba gidanmu bane ina ne nn?” Mami ta fito ta fito da ita snn tace “nan gidansu Aliyu ne” Ikram tace “waye Aliyu” Mami tace “baki san shi ba, wnn mai koya maki Home work” Ikram ta wara ido tana tafa hannu tace “lah yayana, to Mami dama gidanku ba gidansu bne, to shi ba yaron ki bne” Mami bata kuma ce mata komai ba ta ja ta suka shiga babban falon gidan, yan mata biyu da baxa su wuce 14 ba suka tarar xaune falon suna kallon korean Film, duk suka ta so cike da jin dadi suna ma Mami sannu da xuwa, Mami tace “ku dae ba ku gajiya da kallo ina Momynku” dayar da ke rike da remote tace “Momy ta fita amma ynxun nn tace xata dawo Hajiya ce kawae a sama” Mami ta xauna snn ta xaunar da Ikram gefenta tace “to bari in dan jirata, Mujaheed fa” yarinyar tace “ya je raka wani frnd dinsa ynxun nn xae shigo” Mami tace “yauwa gwara ya xo muyi ta ta kare tunda shi bae da mutunci, ina farida da Saiham” dayar yarinyar Aisha da bata ce komai ba tun bayan gaishe da Mami da tayi tace “farida na sama, Saiham kuma taje saloon” Mami tace “to yyi kyau ni ma daga wani wajen nake nace bari in biyo mu gaisa kwana biyu duk ba mu hadu ba” Seeyama tace “Mami ya Khaleel fa yana nn?” Mami tayi murmushi tace “yana nn, baya xuwa nn knn?” Seeyama tace “ae wnn ya khaleel din nn baya son mutane” Mami tayi murmushi kawae, yaran sae kallon Ikram suke, Ikram a hankali tace ma Mami “su waye wa ennan” Mami tace “duk kannin Aliyu ne Ikram” Ikram ta xaro ido tana kallonsu, Wata mata fara da baxa ta wuce Mami bace ta sauko kasa cikin shiga ta alfarma tana dan yamutsa fuska, tana kallon Aisha tace “uban me kike yi a nan Aisha” Aisha ta dan turo baki tace “to Momy ba kallo muke yi ba” ta galla mata harara tace “xo ki wue kar in bata maki rae, bbu TV dakinku ne magulmaciyar bnxa kawae” Mami na kallonta tana mmrshi tace “kwana da yawa Hajiya” Hajiyar ba tare da ta kalleta ba tace “lfya qlau” snn tayi hanyar kitchen tana taka tiles din kmr bata son takawa, Aisha na bubbuga kafa ta wuce sama, seeyama ta tabe baki ta ci gaba da kallonta, Ikram na kallon Mami tace “Mami wacece wnn, ni bana sonta” Mami tayi murmushi tace “mamar Aliyu ce fa” Ikram ta xaro manyan idanunta tace “wnn matar, A’a ba mamarsa bace muguwace wllh” Bude kofa aka yi wani kyakkyawan handsome guy da baxae wuce Khaleel ba ya shigo falon cikin kananan kaya yana danna wayarsa, bae lura da Mami dake xaune falon ba yace “seeyama xo kiyi min transfer don Allah banki sun ki bani kudi kuma ban son fita xuwa siyan kati kawae” kmr ance ya kalli gefensa suka yi ido hudu da Mami dake kallonsa, ya wara manyan idonsa ya juya mata baya da sauri yace “innalillahi,” hanyar stairs yyi da sauri tace “ba sae ka gudu ba Jaheed dawo kawae” tsayawa yyi yana dariya snn ya juya yana kallon Mami yace “amma fa naji kunya Mami don Allah kiyi hkuri tare xamu tafi ma ynxu, jiya ma mun hadu da Khaleel……” ba shiri yyi shiru ya wara manyan idonsa yana kallon Ikram yace “waoww Mami ina kika samo wnn cute Angel din” karasowa yyi da sauri yana kallon Ikram dake kallonsa, Ikram ta juya tana kallon Mami tace “Mami yyi kama da yayana wllh, kalli shima yana da irin abun mu,” ta nuna ma Mami dimple dinta.
[2/25, 08:28] Zjy: ~Ikraam~

Back to top button